Yadda toshewar bututu ke haifar da malalewar bahaya a kasuwar Abuja




Dagwalon bahaya na ci gaba da addabar masu sana’a da kuma masu zuwa cin babbar kasuwar Abuja da ke Unguwar Wuse sakamakon yadda yake malala a wani ɓangaren kasuwar da ya kai tsawon shekara guda.

Mutane da dama da Aminiya ta zanta da su a ranar Talata da ta gabata sun ce, matsalar ta fara ne kamar shekara ɗaya da ta gabata, inda ta shafi wani layi da ke kusa da ɓangaren masu kayan lambu da manyan shaguna na plaza sai kuma bankuna da ke cikin kasuwar.

Ɗaya daga cikin ’yan kasuwar da wakilinmu ya zanta da shi mai suna Zubairu Sulaiman ya ce, sun sha ɗaukar nauyin aikin gyara bututun, amma sai ya sake toshewa bayan wani lokaci.

Ya ce, matsalar da ta faru a baya-bayan nan ta fara ne kamar mako biyu da su ka gabata. Aminiya ta samu labarin cewa, bayan aukuwar matsalar Hukumar Kula da Tsabtar birnin tarayya Abuja ta gabatar da takardan gargaɗi ga ’yan kasuwa da ke ta wajen, inda ta buƙaci da su ɗauki nauyin aikin gyaran cikin kwana biyu ko su fuskanci fushin hukuma.

“Bayan amsar takardar gargaɗin, mun ba da aikin gyaran ga wasu matasa da suka fara aikin gyaran a ranar Asabar da tagabata, sannan suka ci gaba da aikin a ranar Lahadi har zuwa ranar Litinin, amma ba tare da nasarar ƙarasa aikin ba’’, in ji ɗan kasuwa Zubairu.

Ya ce, aikin ya shafi kwasar dagwalon kashin daga cikin mahaɗar bututu sai kuma zungura dogon bututu zuwa cikinsa. Wani ɗan kasuwar mai suna James Ebuka ya ce, matsalar ta sa sun rasa abokan hulɗarsu da dama a sakamkon yadda wajen ke yin ɗoyi.

Ya zargi Hukumar kula da kasuwar ƙarƙashin Ma’aikatar Raya Birnin Tarayya Abuja da nuna halin ko-in-kula a kan matsalar, inda a cewarsa sun fi mai da hankali wajen aikin faɗaɗa gine-ginen shaguna a kasuwar.

Aminiya ta tuntuɓi manajan kula da kasuwar mai suna malam Zubairu Ibrahim, inda ya ce bututun da ke ɗauke da bahayar na haɗe ne da manyan shaguna na plazar da ke kasuwar, wanda da ya ce ba sa ƙarƙashin ofishinsa. Sai dai ya ce, sun sanar da Hukumar Kula da Tsabtar Mmuhalli ta Abuja, inda ya ce tini suka ɗauki mataki a kai.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *