Harin kwara: ‘Sai da ’yan bindiga suka yi awa 10 suna kashe mu kafin jami’an tsaro su zo’




Sarkin garin Woro da ke jihar Kwara, Umar Bio Salihu, ya ce sai da ’yan bindiga suka shafe kusan sa’o’i 10 suna farmakarsu kafin jami’an tsaro su isa yankin domin kai musu dauki.

Hakan, a cewarsa, ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma ƙone ƙauyuka da yawa a yankin.

Salihu, wanda ya yi magana a gidan talabijin na ARISE a ranar Alhamis, ya ce maharan sun fara kai harin ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, amma sojoji sun iso wurin ne da misalin ƙarfe 3 na daren kashegari.

“Na kira waya bayan ƙarfe 5 na yamma, amma ba su zo ba sai ƙarfe 3 na dare. Wannan ya kai kusan sa’o’i 10. Sojoji ba su yi musu farmaki ba, domin sun riga sun tafi kafin su iso,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa babu wani farmakin sama da sojoji suka kai yayin harin.

A cewarsa, al’ummar yankin sun kasance babu kariya tun bayan da aka janye sojoji da ke sansanin yankin, bayan wani hari da aka kai musu watanni uku zuwa biyar da suka gabata.

“Da farko muna da sansanin soja a nan, akwai sojoji kusan 15. Amma bayan da aka kai musu hari, sai aka janye su. Tun daga lokacin babu tsaro a yankin. Wannan ya ba wa ‘yan bindiga damar shigowa duk lokacin da suka ga dama su yi abin da suka so,” in ji shi.

Salihu ya ce maharan na cikin ƙungiyar ta’addanci ta Mamuda, kuma harin ya biyo bayan kin amincewar al’ummar yankin da akidar ƙungiyar.

“Mutanenmu ba su shirya karɓar wannan akida ba. Ina ganin hakan ne ya fusata su suka kai wa ƙauyukan hari,” in ji shi.

Ya kuma musanta ikirarin cewa kisan da aka yi na da alaƙa da addini, yana mai cewa mafi yawan waɗanda aka kashe Musulmai ne.

“Mutanen da suka kashe yawansu Musulmai ne. Kusan kashi 95 cikin 100 Musulmai ne, sai kashi 5 cikin 100 Kiristoci. Ba duka Musulmai ba ne, amma Musulmai su ne mafi rinjaye,” in ji shi.

Sarkin ya ce tun da farko ya riga ya kai rahoton wata wasikar barazana da aka aika masa daga maharan ga jami’an tsaro.

“Da aka kawo min wasikar, aka kawo ta kai tsaye gare ni. A daren nan na aika ta ga DSS a Kiama. Kashegari na kai ta da kaina zuwa majalisar masarauta. Sun yi kwafin takarda. A wannan tsari ina ganin sun rasa hanyar da ta dace. Bayan jami’an tsaro sun yi sintiri, sai ’yan ta’addan suka fusata,” ya ce.

Salihu ya bayyana cewa akalla mutane 75 aka riga aka binne, kuma adadin mutanen na iya ƙaruwa domin har yanzu ana ci gaba da gano gawarwaki a daji.

Ya ƙara da cewa an kone ƙauyuka da dama, ciki har da gidansa.

“Sun ƙone kusan rabin ƙauyukan, ciki har da gidana,” in ji shi.

Salihu ya ce Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ziyarci yankunan da abin ya shafa kuma ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro.

Harin da aka kai a Kwara na cikin jerin hare-haren da ake ta fama da su a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma, inda mazauna yankunan karkara ke fuskantar hare-hare daga ’yan bindiga da ƙungiyoyin ta’addanci duk da ci gaba da ayyukan sojoji.

Tuni dai Shugaban Kasa Bola Tinubu a ranar Laraba ya amince da a gaggauta tura bataliyar sojoji zuwa yankin a ƙarƙashin sabon aikin yaƙi da ta’addanci, inda aka tura sojoji da masu gadin daji domin dawo da tsaro a yankunan da abin ya shafa.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *