Nijeriya Da Faransa Sun Ƙarfafa Haɗin Gwuiwar Tsaro
[ad_1]
Rundunar Sojin Nijeriya da ta Faransa sun ƙara ƙarfafa haɗin gwuiwar tsaro domin yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro. An cimma wannan matsaya ne yayin ganawar Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, da wakilin Tsaron Faransa a Nijeriya, Kanal Stéphane Useo, a shalƙwatar rundunar soji da ke Abuja.
Laftanar Janar Shaibu ya yaba wa Faransa kan ci gaba da tallafa wa Rundunar Sojin Nijeriya, musamman a fannonin musayar bayanan sirri, horaswar ƙwararrun sojoji da kuma ƙarfafa shirin aiki. Ya ce irin wannan haɗin gwiwa na da matuƙar muhimmanci wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar da yankin gaba ɗaya.
- Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa
- Tsaro: Sojoji Sun Gano Masana’antar Ƙera Makamai A Nasarawa
Babban Hafsan ya jaddada aniyar rundunar na ci gaba da inganta ƙwarewar jami’anta a kowane sashi, tare da buƙatar ɗorewar haɗin gwuiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu bisa moriyar juna. Ya bayyana fata ln cewa haɗin gwuiwar ya zama na dogon lokaci da Faransa, musamman a fannin gina ƙarfi da horaswa ta zamani, zai ƙara inganta ingancin ayyukan rundunar.
A nasa jawabin, Kanal Stéphane Useo ya yaba da jajircewa da ƙwazon Rundunar Sojin Nijeriya wajen fuskantar sabbin barazanar tsaro. Ya kuma buƙaci faɗaɗa damar samun manyan kwasa-kwasan soji, musamman a fannonin hulɗa da jama’a da harkokin jiragen sama.
Kanalan ya sake tabbatar da ƙudirin Faransa na zurfafa haɗin gwuiwar tsaro da Nijeriya, yana mai cewa wannan alaƙa na taimakawa wajen samar da zaman lafiya a yankin da kuma ƙarfafa ƙarfin rundunonin ƙasashen biyu.
[ad_2]
Source link