Sauya Sheƙar Abba: A faɗa masa ya ajiye mana kujerar gwamnanmu — Kwankwaso

[ad_1]



Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan yadda rikicin siyasa ke ƙara dagula al’amura a jihar Kano.

Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan lamarin, inda ya buƙaci ’yan siyasa su daina ƙara rura wutar rikicin.

“Wannan lokaci ne mai matuƙar rikitarwa. Abin da ke faruwa a Kano kamar mafarki ne. Da a ce bacci nake yi, idan na farka sai na ga duk ba gaskiya ba ne.”

Kwankwaso ya ce ya yi ganawa da manyan ’yan siyasa domin daƙile yunƙurin da Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf ke shirin yi.

Amma duk da haka ya ce gwamnatin NNPP har yanzu tana da lokaci na yi wa jama’a aiki idan aka samu haɗin kai.

“Na yi magana da duk wanda ya dace na yi magana da shi. Wannan gwamnati har yanzu tana da lokaci, kuma idan muka haɗa kai, mutanen Kano za su amfana.”

Ya gargaɗi masu kira da a koma APC, cewar hakan raini ne ga magoya bayan da suka sadaukar da kansu domin samun nasarar NNPP a Kano.

“Wasu suna cewa mu bar nan mu shiga ‘Gandujiyya’. Yanzu an rabu gida a Kano, tsakanin gaskiya da akasin haka.”

Kwankwaso ya ce magoya bayan tafiyar suna cikin tsaka mai wuya, amma duk da haka sun nuna haƙuri da jajircewa.

“Mutane da yawa suna cikin raɗaɗi. Wasu sun kamu da rashin lafiya, wasu suna cikin ruɗani, amma har yanzu suna tsaye daram saboda sun yi imani da wannan tafiya.”

Ya kuma tambayi dalilin da ya sa ake matsa wa Kano lamba duk da cewa APC na riƙe da yawancin jihohin ƙasar nan.

“Idan suna da gwamnoni da yawa, me ya sa dole sai Kano? Su yi hattara, kada su raina mu.”

Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa tilasta wa gwamnan Kano ya sauya sheƙa zai zama ƙwace ikon gwamnati ne.

“Idan suna so ya tafi, su faɗa masa ya ajiye kujerar gwamna ya tafi. Shi kaɗai ne gwamnan da muke da shi.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *