Sirrin Kasar Sin Na Fitar Da Al’ummunta Daga Kangin Talauci
[ad_1]
A kwanakin nan, wata jami’a da ke kula da ayyukan tallata amfanin gona ta jihar Xinjiang da ke arewa masu yammacin kasar Sin ta rasu sakamakon mummunan raunin da ta ji a sanadin fadowarta daga doki, a lokacin da take daukar shirin bidiyo na tallata amfanin gona, lamarin ya janyo hankalin al’ummar kasar Sin sosai, kuma masu bibiyar shafinta da yawa sun yi ta rubuta kalamai na jimami a hotunan bidiyon da ta wallafa, inda suka ce, “Ke ce kika fahimtar da al’ummun kasar Sin game da gundumar Zhaosu, har da yankin Yili da ma kykkyawar jihar Xinjiang baki daya.” “Sakamakon kokarinki, rayuwar manoma da makiyaya ta kyautata”.
Sunan jami’ar shi ne He Jiaolong. A shekarar 2020, malama He Jiaolong wadda a lokacin ke kan kujerar mataimakiyar shugaban gundumar Zhaosu, ta fara tallata amfanin gona na wurin ta shafinta na sada zumunta. A daidai waccan shekara kuma, wani hoton bidiyon da ta dauka game da yadda take hawan doki da ke gudu a filin da dusar kankara ta rufe, sanye da jar riga, ya yi matukar samun farin jini daga masu ziyartar shafukan yanar gizo, lamarin da ya sa ta yi suna, har ma gundumar Zhaosu ta fara janyo hankalin al’umma. A shekarar 2021, yawan baki masu yawon shakatawa da ke zuwa gundumar Zhaosu ya ninka na baya har sau da dama.
Duk da haka, malama He Jiaolong ba ta taba kallon kanta a matsayin tauraruwa ba. Ta ce, burinta shi ne fatan ganin masu bibiyar shafinta za su fara mayar da hankalinsu a kan gundumar Zhaosu bisa hotunan bidiyon da ta wallafa, don janyo karin baki masu yawon shakatawa tare da sayar da amfanin gona na gundumar zuwa sassa daban daban na kasar Sin. Sau da yawa malama He Jiaolong ta ce, “Yadda aka ilmantar da mu, ba don mu fita daga garuruwanmu da ke fama da talauci ba ne, sai dai don mu yi kokarin fitar da garuruwan daga kangin talauci da suke ciki.”
Jihar Xinjiang yanki ne da Allah ya albarkace shi da ni’imtaccen yanayi da ma wadatattun amfanin gona. A cikin ’yan shekarun baya, malama He Jiaolong ta dukufa wajen yayata al’adu da gabatar da bayanan da suka shafi wuraren yawon shakatawa na jihar, da ma tallata amfanin gona na wurin. Tun daga shekarar 2020, malama He Jiaolong tare da sauran ma’aikata da ke tallafa mata, sun yi ta tallata amfanin gona na jihar Xinjiang ba tare da samun ladan aikin ba, don taimaka wa manoma sayar da amfaninsu, matakin da kuma ya samar da karin guraben aikin yi ga al’ummar wurin. Daga shekarar 2021 har zuwa 2024, malama He Jiaolong ta wallafa hotunan bidiyo 628, tare da gudanar da tallan kayayyakin amfanin gona ta bidiyo kai tsaye har sau 396, inda kudin cinikin da aka yi bisa tallar ta ya kai Yuan miliyan 360, kwatankwacin dala kimanin miliyan 52. Shafinta ya yi ta tattara kayayyaki masu inganci na sassan jihar Xinjiang, tare da sayar da su zuwa sassa daban daban na kasar Sin, matakin da ya samar da karin kudin shiga ga manoma da ma karin guraben aikin yi ga al’ummar yankin.
A karshen shekarar 2020, kasar Sin ta cimma burin da ta sanya gaba na saukaka fatara, inda aka fitar da al’ummu kimanin miliyan 989.9 da ke yankunan karkara, da gundumomi 832, da kuma kauyuka dubu 128 daga kangin talaucin da suke ciki, shekaru 10 ke nan kafin a cimma burin saukaka fatara na MDD, bisa ajandarta ta tabbatar da dauwamammen ci gaba ta zuwa shekarar 2030. A lokacin, akwai abokaina ’yan Afirka da suka min tambaya, shin ta yaya kasar Sin ta cimma wannan gagarumar nasara? A ganina, hakan ya tabbata ne sakamakon kokarin da aka yi ta fannoni da dama, kuma ba shakka, jami’ai a mataki na farko irinsu malama He Jiaolong sun ba da babbar gudummawa.
Raya sassa daban daban bisa mabambantan yanayin da suke ciki, da kuma kirkire-kirkire su ne bakin zaren warware matsalar tabbatar da ci gabansu, kuma muna iya gano hakan ne daga yadda gundumar Zhaosu ta dogara ga ni’imtaccen yanayi, da ma albarkatun dabbobin kiwo da take da su wajen raya sana’o’i na musamman, da ma yadda malama He Jiaolong ta yi kirkire-kirkire wajen tallata amfanin gona na wurin.
Malama He Jiaolong ta rasu, amma ruhinta zai dore. Domin jama’a ake saukakawa fatara, kuma ana dogara ga jama’a wajen saukaka fatara, baya ga haka, rikon gaskiya da raya sassa daban daban bisa mabambantan yanayin da suke ciki, duk wadannan sun kasance dabarar kasar Sin wajen saukaka fatara, wanda hakan zai haskakawa kasashen duniya hanyar fitar da kansu daga talauci.
[ad_2]
Source link