Bayan shekara 12 an kama wanda ake zargi da kashe jami’an NDLEA 3
[ad_1]
Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), sun kama wani ƙasurgumin dilan ƙwaya mai suna Lekan Jimoh, wanda aka fi sani da “Kanmo-kanmo”, bayan ya shafe shekaru 12 ana nemansa ruwa a jallo.
Hukumar nemansa ne bisa zarginsa da hannu a kisan jami’an NDLEA uku.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce an kama Jimoh ne a ranar Juma’a a maɓoyarsa da ke Owode, a Jihar Ogun, bayan samun bayanan sirri.
A lokacin kamen, jami’an sun same shi da kilogiram 69 na tabar wiwi.
Babafemi, ya ce kamen ya nuna ƙudirin NDLEA na tabbatar da cewa babu wani mai laifi da zai tserewa hukunci.
A cewar NDLEA, Jimoh yana daɗe yana aikata laifuka.
A ranar 15 ga watan Yuni, 2014, ya jagoranci kai wa jami’an NDLEA da suka zo kama shi hari.
A wannan lokaci an kashe jami’ai uku ciki har da Rabiu Usman Kazaure.
Ko da yake ya tsere a wancan lokaci, hukumar ba ta samu damar kama shi ba.
NDLEA ta ƙara bayyana cewa a ranar 12 ga Agustan 2023, jami’anta sun kai samame gidansa da ke Ado-Odo, a Jihar Ogun.
Duk da cewa ya tsere a karo na biyu, jami’an sun ƙwato buhu 139 na tabar wiwi da nauyinsu ya kai kilogiram 1,922.
Bayan kammala shari’ar ƙwace kadarori a kotu, an ƙwace gidan da yake amfani da shi wajen adana miyagun ƙwayoyi, kuma an miƙa shi ga Gwamnatin Tarayya.
NDLEA ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an yi wa jami’anta adalci tare da kare ƙasa daga laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link