Katanga ta kashe yara 5 a Maiduguri
[ad_1]
Wata katangar gida da ta rushe a unguwar Bulumkutu da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno, ta kashe yara biyar, yayin da yaro ɗaya ya ji munanan raunuka.
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa yaron da ya ji rauni yana karɓar magani a yanzu, yayin da aka fara bincike kan musabbabin rushewar.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a jihar, ASP Nahum Daso, ya ce rundunar ta samu rahoton wannan hatsari da misalin ƙarfe 8:00 na daren Lahadi ta hannun jami’in ’yan sandan da ke kula da sashen Bulumkutu.
“Da misalin ƙarfe 8:00 na dare, mun samu rahoto daga jami’in ’yan sandan sashen Bulumkutu cewa wata katanga ya fadi kan yara shida,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa biyar daga cikin waɗanda abin ya shafa, waɗanda duk ba su kai shekaru 16 ba, sun mutu nan take, yayin da yaro na shidan ya samu raunuka kuma ana kula da shi a babban asibitin gwamnatin jiha na kwararru da ke Maiduguri.
“Aiki na farko da rundunar ta yi shi ne fara bincike nan take kan rushewar ginin da sauran batutuwan da suka shafi yanayin yaran a cikin al’ummar Bulumkutu,” in ji shi.
Ya ce suna son gano ko akwai wani aikin sakaci ko kuma duk wani abin da ya shafi lamarin.
ASP Daso ya yi kira ga jama’a da su bi ƙa’idojin gini tare da shawartar iyaye da masu kula da yara da su sa ido sosai kan ’ya’yansu da unguwanni, musamman a cikin gidaje.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link