’Yansanda Sun Ceto Yara 4 A Jihar Nasarawa

[ad_1]

Rundunar ’yansandan Jihar Nasarawa ta ceto wasu yara huɗu da aka sace tare da mayar da su hannun iyayensu.

’Yansanda sun ce sun ɗauki matakin ne bayan samun rahoto a ranar 31 ga watan Disamba, 2025, kan ɓacewar yaran a yankin New Nyanya da ke Ƙaramar Hukumar Karu.

  • Sojoji Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
  • Sojoji Sun Tarwatsa Gungun Masu Tayar Da Bam A Adamawa

Bayan samun rahoton, rundunar ta fara bincike.

Haɗin gwiwar rundunar ’yansandan Babban Birnin Tarayya tare da na bayanan sirri, jami’an tsaro sun gano maɓoyar waɗanda ake zargi inda suka ceto yaran cikin ƙoshin lafiya.

’Yansandan sun ce ana zargin Abraham Asoje mai shekaru 28 da Joy Bolaje mai shekaru 29 da hannu wajen sace yaran tare da tsare su.

Sauran waɗanda ake zargin sun tsere, kuma ana ci gaba da nemansu.

Kwamishinan ’yansandan jihar, Shetima Mohammed, ya yaba da ƙwarewar jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar wa al’umma cewa rundunar ’yansanda za ta ci gaba da kare rayuka, musamman yara da sauran masu rauni a jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *