Yawan Wasiku Da Kunshin Sakwanni Da Aka Yi Jigilarsu Ta Gidan Wayar Kasar Sin Ya Kai Biliyan 216.5 A Shekarar 2025

[ad_1]

A shekarar 2025 da ta gabata, yawan wasiku da kunshin sakwanni da aka yi jigilarsu ta gidan wayar kasar Sin, ya kai biliyan 216.5, adadin da ya karu da kaso 11.5 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabace ta. Daga cikin adadin, hidimar jigilar kayayyaki na gaggawa ta kai biliyan 199, wanda ya nuna karuwar kaso 13.7 bisa dari.

Da safiyar yau Laraba ne hukumar gidan waya ta kasar Sin ta labarta hakan, a gun taron ayyukan gidan waya na 2026. Yayin taron, daraktan hukumar Zhao Chongjiu ya bayyana cewa, a shekarar 2025, kudaden shiga na ayyukan gidan waya na kasar ya kai Yuan tiriliyan 1.8, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 6.4 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabaci hakan. Daga cikin adadin, kudaden shiga na hidimar jigilar kayayyakin na gaggawa ya kai Yuan tiriliyan 1.5, wanda ya karu da kaso 6.5 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2024.

Zhao ya kara da cewa, “Ayyukan na ci gaba da bunkasa cikin lumana, kuma manyan ma’aunai sun ci gaba da karuwa ba tare da tangarda ba, matakin dake habaka ci gaban tattalin arziki da zamantakewa sosai”. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *