HOTUNA: Kamfanin Media Trust ya buɗe sabon babi na aikin jarida a zamanance

[ad_1]



Kamfanin Media Trust, mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya, haɗi da rassansa biyu na gidan talabijin da rediyo — Trust TV da Trust Radio — ya buɗe sabon babi na aikin jarida a zamanance.

A ƙarƙashin wani shiri da ya yi wa laƙabi da Project Evolution, domin inganta sahihin aikin jarida a zamanance, Kamfanin Media Trust, a wannan Larabar, ya ƙaddamar da sabon ɗakin gudanar da ayyukan labarai na dijital, wato Digital Newsroom a hedikwatarsa da ke Abuja.

Da yake jawabi a yayin buɗe sabon babin, Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin, Malam Ahmed Shekarau, ya ce an dashen ƙwan wannan gagurmin aiki da ya samo asali tun 2006, kuma naɗin Malam Naziru Mikail a matsayin Daraktan Ayyukan Dijital a 2019 ya taimaka wajen cimma nasarar wannan sabuwar ƙyanƙyasa da kamfanin ya yi.

Shi ma Daraktan Edita, Malam Ibrahim Shehu, ya bayyana ɗakin labaran a matsayin irinsa na farko a Yammacin Afirka da ya haɗa jarida, rediyo, talabijin da kafafen dijital a wuri guda, tare da amfani da fasahar zamani da kuma ƙirƙirarriyar basira wato AI.

Da yake nasa tsokacin, jagoran masu bayar da shawarar da ta kai ga cimma wannan nasarar, Juan Senor, ya ce ɗakin labaran na dijital zai taka muhimmiyar rawar gani wajen ƙarfafa ayyukan ’yan jarida da ke aiki a kamfanin, amma ba maye gurbinsu zai yi ba.

Shugaban mamallaka kamfanin, Malam Kabiru Yusuf, ya ce wannan zakaran-gwajin-dafi da kamfanin ya zama tsakanin sa’o’insa alama ce ta cikar burin da aka assasa shi, tun tsawon shekaru 25 da suka gabata.

Hotunan sabon ɗakin labaran na dijital da aka ƙaddamar

Malam Kabiru Yusuf
Ahmed Shekarau yana jawabi
Daraktoci, Manajoji da sauran ma’aikatan kamfanin yayin ƙaddamar da sabon ɗakin gudanar da ayyukan labarai
Malam Ibrahim Shehu


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *