Yadda Mota Ta Kashe Mutane 3, Ta Jikkata 40 A Yobe
An tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da wasu kimanin 40 suka samu raunuka daban-daban bayan da wata babbar mota ta ƙwace ta afka cikin cunkoson mutanen da ke zaune a gefen hanya a kan hanyar Gombe zuwa Potiskum a jihar Yobe.
Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na rana a ranar Laraba kusa da garin Badejo a karamar hukumar Potiskum ta jihar Yobe.
- Majalisa Ta Yaba Wa ‘Yansanda Kan Gaggawar Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kisan Gilla A Kano
- Darajar Tamburan Kasar Sin Sun Karu A Duniya
Shaidu sun ce, babbar motar tana sharara gudu ne inda ta ƙwace a hannun direban sannan ta yi kan mutane da dama da ke zaune a gefen hanya.
Kwamandan Rundunar Tsaron Hanya a Jihar Yobe (FRSC), Paul Andrew, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa, binciken farko ya gano cewa, maƙare mota da kaya mai yawa, da gudu mara misali ne ya haifar da hatsarin.