Sanata Rufai Hanga ya umarci tsoffin shugabannin NNPP su dawo da motocin da ya ba su tun da sun koma APC
[ad_1]
Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, ya umarci tsoffin shugabannin Jam’iyyar NNPP na ƙananan hukumomin mazaɓarsa da su dawo da motocin da aka ba su tun da sun sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC.
Umarnin, wanda aka aika ta wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sakataren ofishin Sanatan, Injiniya Ibrahim Nakwalli Kawaji, ya bayyana cewa motocin da aka raba domin ayyukan jam’iyyar NNPP a kananan hukumomi, dole ne a dawo da su zuwa ofishin Sanatan da ke titin Sokoto Road da ke Ƙaramar Nasarawa tsakanin 28 zuwa 30 ga Janairu, 2026.
Wasiƙar ta ce motocin za su kasance a ofishin Sanatan har sai an warware rikicin cikin gida na jam’iyyar, tare da kira ga shugabannin da su ci gaba da yi wa jam’iyyar hidima da aminci.
Rahotanni sun nuna cewa umarnin ya shafi dukkan shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi da ke Kano ta Tsakiya, ciki har da Dala, Dawakin Kudu, Fagge, Garun Mallam, Gezawa, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kura, Madobi, Minjibir, Nasarawa, Tarauni, Ungogo da Warawa.
Wasiƙar ta ƙara da cewa dole ne a miƙa motocin kai tsaye ga shugaban ofishin Sanatan, Alhaji Shehu Tijjani Usman Tarauni, tare da jaddada cewa motocin mallakin jam’iyya ne.
A makon da ya gabata ne Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka zuwa APC tare da ’yan majalisar dokokin jiha 22, ’yan majalisar wakilai 8 da dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Wannan mataki ya kawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyun.
Wani mai amfani da kafafen sada zumunta, Sani Gilashi Haruna, ya soki umarnin, yana cewa ba shi da tushe a tarihin siyasar Kano.
Ya tuna yadda fitaccen ɗan siyasa, Alhaji Abdussalam Abdulkarim (AA Zaura), ya raba motocin ga shugabannin jam’iyya a dukkan ƙananan hukumomi ba tare da neman a mayar da su ba bayan faduwar zabe.
AA Zaura ma ya bayyana cewa idan Sanata Hanga ya nace kan karɓar motocin, shi kuma zai samar da sabbin motocin da suka fi inganci ga shugabannin jam’iyyar.
Kakakinsa, Malam Dahiru Ahmad Maihuddadu, ya ce wannan mataki na Sanatan abin takaici ne.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link