Ƙarfafa wasannin gargajiya zai hana matasa aikata laifi — ALGON
[ad_1]
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), ta yi kira ga Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu Rubuta Labaran Wasanni (SWAN) da ta ƙara mayar da hankali wajen yada labarai kan wasannin gargajiya, irin su langa da kokawa.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe wanda shi ne shugaban ALGON reshen Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin SWAN na jihar suka kai masa ziyarar ban girma, inda suka nemi goyon bayansa kan babban taron bita da ƙungiyar ke shirin gudanarwa.
A cewarsa, ƙara bayar da muhimmanci ga wasannin gargajiya zai taimaka wajen jan hankalin matasa zuwa harkokin ci-gaban rayuwa, tare da rage yawan fadawa cikin laifuka da shan miyagun ƙwayoyi.
Ya kuma shawarci SWAN da ta ƙulla alaƙa da Hukumar Ci-gaban Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) domin haɗa kai wajen yada labarai kan wasannin da ake gudanarwa a yankunan ƙarƙara.
Shugaban na ALGON ya tabbatar da cewa ƙungiyarsa za ta ci gaba da tallafa wa SWAN da kuma sauran shirye-shiryen wasanni da suka dace da manufofin gwamnati a jihar.
A nasa jawabin, Sakataren SWAN na jihar, Williams Attah, wanda ya wakilci shugaban ƙungiyar, Mark Nuhu Mabudu, ya gode wa shugaban ALGON bisa alƙawarin goyon baya, tare da tabbatar da cewa ƙungiyar za ta haɗa kai da shi a cikin shirye-shiryenta.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link