’Yan bindiga sun sace Fasto, sun hallaka mutum 3 a Kaduna

[ad_1]



Wasu ’yan bindiga sun sace Faston wata coci, mai suna Rabaran Fr. Nathaniel Asuwaye, tare da wasu mutum 10a ƙauyen Karku da ke Ƙaramar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna.

An sace Faston ne a gidansa da misalin ƙarfe 3:20 na safiyar ranar Juma’a.

Shi ne limamin Cocin Katolika ta Holy Trinity da ke ƙauyen Karku.

A wata sanarwa da Cocin Katolika ta Kafanchan ta fitar, wadda Babban Sakataren cocin, Rabaran Fr. Jacob Shanet, ya sanya wa hannu, ta yi Allah-wadai da harin.

Sanarwar ta ce a lokacin harin, ’yan bindigar sun kashe mutane uku.

Mutanen da suka rasa rayukansu sun haɗa da Jacob Dan’azumi, Maitala Kaura da Alhaji Kusari.

Wasu mazauna ƙauyen sun ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyen ne da daddare, inda suka dinga harbe-harbe, kafin su sace Faston da sauran mutanen, sannan suka tafi da su.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan harin.

Cocin ta roƙi mabiyanta da sauran jama’a da su yi addu’a domin samun nasarar kuɓutar Faston da sauran waɗanda aka sace cikin lafiya.

Mazauna ƙauyen Karku su yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga.

Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *