Hukumar Siyasa Ta Kwamitin Kolin JKS Ta Kira Taro Don Bitar Rahoton Binciken Yankuna
[ad_1]
Hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS ta kira taro a yau Juma’a 28 ga watan Nuwamban nan don duba cikakken rahoton binciken da kwamitin kolin JKS karo na 20 ya yi a larduna da yankuna masu cin gashin kansu da manyan birane. Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron.
Taron ya nuna cewa, kwamitin wanda ke karkashin jagorancin Xi Jinping, ya ba da muhimmanci sosai ga aikin binciken, ya kuma tsara shirin gudanar da bincike a zagaye na biyar da na shida, don kammala binciken a dukkannin larduna da birane. Daga binciken, an samu sabbin ci gaba da nasarori kan ayyukan larduna da birane, ko da yake akwai wasu matsaloli, wadanda dole ne a ba da muhimmanci sosai ta fuskar siyasa, a kuma magance su bisa iyakacin kokari.
Taron ya jaddada cewa, ya kamata a yi amfani da sakamakon binciken yadda ya kamata, a yi nazari mai zurfi don magance matsalolin da binciken ya gano, a inganta gyare-gyare mai zurfi, da kuma ci gaba da magance matsaloli daga tushe. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link