Vinicius zai dawo kan ganiyarsa — Bellingham

[ad_1]



Jude Bellingham, ɗan wasan tsakiyar Real Madrid, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa abokin wasansa, Vinicius Junior zai shawo kan matsalar ƙamfar cin ƙwallo da yake fama da ita, gabanin wasan daf da na kusa da na ƙarshe na Spanish Super Cup da Atletico Madrid.

Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid ne a Jeddah ranar Alhamis, inda take neman tsallakawa wasan ƙarshe da za ta haɗu da Barcelona ko Athletic Bilbao.

Kawo yanzu dai Vinicius bai zura ƙwallo a raga ba tun wasanni 15 da suka gabata a dukkan gasa, inda ƙwallayensa na ƙarshe suka zo ne tun watan Oktoba.

Sai dai duk da haka, Bellingham ya ce har yanzu ɗan wasan Brazil ɗin na taka rawar gani sosai a ƙungiyar.

Bellingham ya bayyana cewa Vinicius na fuskantar matsin lamba mai yawa, ba wai a matsayinsa na ɗan wasa kaɗai ba, har ma a matsayinsa na mutum, wanda hakan ke shafar yadda yake nuna fushi ko damuwa a fili yayin wasa.

Ya ce duk da rashin cin ƙwallo, Vinicius har yanzu ɗan wasa ne mai iya ƙirƙiro barazana a kowane lokaci, yana mai jaddada cewa ba jefa ƙwallo kaɗai ke nuna ƙoƙarin ɗan wasa ba.

Bellingham ya ƙara da cewa ‘yan wasan Real Madrid gaba ɗaya suna goyon bayan Vinicius, musamman ganin irin gudunmawar da yake bayarwa idan yana cikin karsashi.

“Idan yana cikin ƙoshin lafiya da ƙwarin gwiwa, Real Madrid na ƙara ƙarfi sosai,” in ji shi, yana mai tabbatar da cewa Vinicius zai dawo kan ganiyarsa nan ba da jimawa ba.

Har ila yau, Bellingham ya ce ‘yan wasan suna tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan koci Xabi Alonso, duk da jita-jitar korar sa a ƙarshen shekarar 2025 sakamakon rashin katabus.

Ya ce a Real Madrid ana yawan ƙara girman matsala fiye da yadda take, amma duk da haka ‘yan wasa na tare da mai horaswa a kowane hali.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *