Gwamnan Filato ya fice daga PDP zai koma APC




Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya fice daga Jam’iyyar PDP a hukumance kuma yana shirin komawa jam’iyyar APC ranar Juma’a.

Hakan na zuwa ne makonni biyu kacal bayan shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa Gwamnan ya koma APC.

An yi ta ce-ce-ku-ce game da shirinsa na komawa Jam’iyyar APC, amma da sanarwar Yilwatda, an warware duk wasu batutuwan da suka taso.

A wasiƙar murabus ɗin mai kwanan wata 29 ga watan Disamba, 2025, wacce aka aike wa shugaban Jam’iyyar PDP na gundumar Ampang ta Yamma, Ƙaramar hukumar Mangu ta jihar, Gwamna Mutfwang ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ba tare da ɓata lokaci ba.

“Na rubuta murabus ɗin ne domin in sanar da ku cewa na fice daga jam’iyyar PDP nan take,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa, “Idan aka yi la’akari da haƙiƙanin abin da ke faruwa a wannan lokaci, da kuma jagorancin da na yi na samar da jagoranci mai ma’ana, da bayyananniyar alƙibla, da isar da shugabanci mai inganci, ya tilasta min neman wata hanyar siyasa ta daban don shiga harkar siyasa,” in ji shi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *