Illolin Tsarki Da Sabulu Ga Mace

[ad_1]

Bisa kyakkyawan zato, mafi yawan mata kan yi tsarki da sabulu ne da manufar tsaftace jikinsu, sai dai, kash, rashin sani ya sa su ke aikata hakan, domin da sun san irin lahanin da ya ke mu su da ba su yi tsarki da sabulu ba.

Wani ƙwararren likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Ibadan, Imran Morhason-Bello, ya ce, wasu abubuwa da mata ke aikata wa cikin rashin sani, kamar amfani da turare ko sabulu a gaba, na sa su kamuwa da cota.

  • Manyan Jami’o’in Kasar Sin Sun Samar Da Karin Guraben Karatu 38,000 Cikin Shekaru Biyu Da Suka Gabata
  • CMG Zai Watsa Shirin Nishadantarwa Na Murnar Bikin Zhongqiu Gobe Da Dare

Saboda da haka sai Likita ya shawarci ‘yan uwa mata kan su guji yin amfani da sabulu ko turare a gabansu da nufin tsaftace wajen, don kuwa a maimakon gyara hakan na iya janyo mu su mummunar illa, inda zai haifar da rashin jin daɗin.

Dokta Morhason-Bello, ya ba da wannan shawara ne a wata makala da ya gabatar wajen wani taro da aka gudanar da nufin dakile al’adar yi wa mata kaciya a Najeriya.

Taron, wanda Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta shirya tare da taimakon Ƙungiyar (UNPFA) ta majalisar ɗinkin Duniya, da Jami’ar Ibadan ta gudanar da shi ne a birnin tarayyar ƙasar nan, Abuja.

Kwararren likitan ya bayyana cewa, ba kaciyar mata ce kawai ke haifar da mummunar illa ga al’aurar mata ba wajen jin gyara mace, har ma da amfani da sabulu ko turare da mata ke yi da nufin tsaftace al’aurarsu ko kuma amfani da wasu magungunan kayan mata.

Ya ce, lokacin da mace ta saba da yin amfani da sabulu ko turare wajen tsaftace gabanta, ko kuma yin amfani da magungunan kayan mata, to sannu kan hankali hakan zai yi tasiri a gabanta, sannan daga bisani sai ya yi mata mummunar illa ta hanyar haifar mata cuta

A cewarsa, “fatar jikin dan-tsakan mace da ta tsakiya jikinta ba ta da kauri, kuma cike suke da jijioyoyin jini ma su yawan gaske, sakamakon yawan amfani da sabulu ko turare ko kuma kayan mata da mata ke yi, sai fatar ta dunƙule ta gaza kai sako ga kwakwalwa a karshe sai hakan ya haifar wa da mace cutar ciwon sanyi.

Dokta Morhason-Bello ya ƙara da cewa, domin ƙubuta daga wannan matsala, dole ne mata su guji cusa magungunan kayan mata, ko kuma sanya magungunan zamani ba tare da iznin likita ba, hakanan su guji yin amfani da turare, ko sabulu, saboda hakan zai hana su sakewa, baya ga haka ma zai iya haifar mu su da cututtuka.

“A gaskiya, wasu daga cikinsu na amfani da hannayensu wajen cusa waɗannan magungunan cikin jikinau , abin da ba su sani ba shine, idan su ka ɗauki tsawon lokaci su na aikata hakan, sai ya haifar mu su da matsewar jikinsu fiye da kima. Mun sha samun matsalolinan.

“Idan mace ta samu kanta cikin wannan matsala, don warkar da ita akwai buƙatar a yi ma ta aikin tiyata nau’i daban-daban ko kuma ayi koƙarin samar ma ta da wata saban waje. Kafin a samu nasarar hakan kuma dole matar ta zauna a asibiti tsawon watanni ma su yawa.

“Saboda haka, abin da ya fi dacewa ga mace don tsaftace jikinta shine ruwa mai tsabta kawai. Idan ta yi amfani da duk wani abu da yake ɗauke da wani sanadari kamar sabulu ko turare, zai iya kashe kwayoyin halittar da Ubangiji ya halitta mata don jikinta ya zauna lafiya.

Amma yayin da ta lahanta ƙwayoyin halittar da Ubangiji ya yi mata, sai ƙwayoyin cuta su samu damar shiga jikinta. A ƙarshe irin waɗannan mata za su fara fitar da gurbataccen ruwa, “inji shi.

Ya ci gaba da bai wa mata shawarar cewa, kama ta ya yi su ke wanke jikinsu da ruwa mai tsafta kaɗai, kuma “kar mata su damu da wani wari da ke fita daga jikinsu saboda wannan warin dabi’ar da Allah Ya halicci wajen ne, matuƙar ba wari ne na cuta ba, wanda shi kuma warin cuta ya na kasancewa mai yawa ne”.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *