Za A Miƙa Ɗaliban Kebbi Da Aka Ceto Ga Iyayensu — Gwamna Idris

[ad_1]


A yau Laraba ake sa ran gwamnatin Jihar Kebbi za ta miƙa ɗaliban makarantar ’yan mata ta Maga da aka sace makon jiya ga iyayensu.

An ceto ɗaliban ne daga hannun ’yan bindiga a ranar Talata.

Gwamna Nasir Idris ya ce an bi umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gaggauta kuɓutar da yaran, wanda har ya tura ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, zuwa jihar.

Gwamnan ya tabbatar wa iyaye cewa an samu yaran cikin ƙoshin lafiya:

  • Ya ce jami’an tsaro sun gano inda yaran suke suka ceto su.
  • Ya kuma ce babu kuɗin fansa da aka biya domin a sako ɗaliban.
  • Gwamnatin jihar ta ce za a miƙa yaran ga iyayensu su koma gida.

’Yan bindigar sun sace ɗalibai 25 daga makarantar Maga ne a makon da ya gabata bayan sun kashe mutane biyu.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake fama da sace-sacen mutane a jihohin Neja, Kwara, Sakkwato da Kano, lamarin da ya tayar da hankali a ƙasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *