Yawan Cin Namijin Goro Na Hana Maza Haihuwa

[ad_1]

Bincike ya tabbatar da cewa, muddin aka jima ana amfani da namijin goro; babu shakka hakan ka iya kawo barazana ga ƙwayoyin halittar da suke taimakawa wajen haihuwa. Ma’ana, rashin samun haihuwa.

Mutane da dama na amfani da namijin goro tare da sanya wa a ransu cewa, sakamakon sinadarin da namijin goron ke ɗauke da shi; zai iya taimaka wa maza wajen ɗanɗano ko gamsar da iyalansu yayin saduwar aure, wanda a gefe guda kuma yana barazana ga ƙwayoyin halittar da suke taimakawa wajen haihuwa.

  • Jagororin Kasar Sin Sun Halarci Bikin Gala Na Sabuwar Shekara Da Ya Kunshi Wasan Opera Na Gargajiya
  • Gwamnatin Katsina Ta Kare Shirinta Na Sakin Ƴan Ta’adda 70 Daga Gidan Yari

A dukkanin binciken da suka gabata, sun tabbatar da cewa; sinadarin namijin goro, ba ya ƙara wa ɗa namiji kuzari ko ƙarfin sha’awa ko kuma maganin mazakuta, hasali ma, daɗewa ana yin ta’ammali ko cin namijin goron ba bisa ƙa’ida ba, yana iya haifar wa da ɗa namiji matsalar rashin haihuwa.

Haka nan, namijin goro yana ɗauke da sinadarin da ke taimakawa wajen narkar da abinci, yana kuma taimaka wa jikin mutum wajen fitar da ƙwayoyin cutar da jiki bai san su ba ko kuma waɗanda za su iya lalata garkuwar jiki.

Haka zalika, namijin goro, na da sinadarin da ke taimakawa wajen ganin jiki ya samu waraka a ɓangaren kumburi tare da rage yawan kitsen da ke tattare a jikin Ɗan’adam ya kuma sa kitsen ya ragu ya yi daidai wadaida a jikin mutum.

Bugu da ƙari, Namijin goro na ɗauke da sinadarin da ke maganin abubuwan da ke da alaƙa da Maleriya ko ciwon siga, wanda ka iya yin maganin zazzaɓin cizon sauro, inda a wani ɓangaren ma ake ganin kamar ya fi alfanu ga masu ciwon siga; ta hanyar daidaita sigan, musamman idan ya yi yawa a jikin mutum.

Har ila yau, namijin goro na ɗauke da sinadarin da ke bunƙasa garkuwar jiki, ma’ana yana da abin da ake kira a turance ‘antioɗidant’. A taƙaice, namijin goro na ɗauke da sinadarin da zai iya tallafa wa jikin Ɗan’adam, ya fitar da abin da ka’iya zama guba ko wani abu makamancin haka a jikinsa.

Kazalika, namijin goro yana taimaka wa garkuwar jikin Ɗan’adam, musamman wajen buɗe ƙofofin huhu, hanyoyin iska; wanda Ɗan’adam, galibi mai fama da matsalar cutar asma ko fitar da numfashi, kan iya samun waraka idan ya yi amfani da shi.

Don haka, a nan yana da kyau a fahimci cewa; Namijin goro na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar Ɗan’adam, amma a gefe guda kuma idan ya yi yawa, ma’ana; idan aka fiye amfani da shi, ta hanyar cin sa a kullum, musamman maza za su iya fuskantar matsalar rashin haihuwa.

Mun ɗauko wannan ne daga daga tattaunawar da BBC ta yi da Dakta Auwal Musa Umar

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *