‘Yansanda Sun Kama Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wata Mata Da ‘Ya’yanta 6 A Kano
[ad_1]
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta sanar da kama miyagun mutane uku da ake zargi da kisan gillar wata mata da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi, cikin birnin Kano a ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yansanda (PPRO), CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi, rundunar ta ce an kama wadanda ake zargin ne a karkashin kulawar Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori.
“Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kano ta yi amfani da jami’an leken asiri don kama wasu mutane uku da ake zargi da kisan gillar wata mata da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi, Kano a ranar 17 ga Janairu, 2026,” in ji sanarwar.
[ad_2]
Source link