Mark Zuckerberg Zai Gurfana A Gaban Kotu A Amurka

[ad_1]

Shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg, zai je kotu a birnin Los Angeles a ƙasar Amurka nan ba da daɗewa ba.

Ana tuhumarsa ne saboda damuwar yadda shafukan sada zumunta ke shafar rayuwar mutane.

  • Su Yiming Ya Samarwa Kasar Sin Lambar Zinare Na farko A Gasar Olympic Ta Lokacin Hunturu
  • Mutum 37 Sun Mutu, 25 Sun Jikkata Sakamakon Shaƙar Iskar Guba A Ramin Haƙar Ma’adinai A Filato

Wannan shi ne karon farko da wanda ya kafa Facebook zai amsa tambayoyi a kotu game da tasirin Instagram, wanda kamfanin Meta ya mallaka, kan lafiyar ƙwaƙwalwar matasa.

Idan kamfanin ya yi rashin nasara a shari’ar, hakan na iya jawo masa babbar matsala, domin zai iya sa mutane da yawa su fara kai ƙara a kansa.

Wadda ta kai ƙarar ta ce ta samu matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa ne saboda yadda ta saba da amfani da Instagram da kuma YouTube mallakin Google tun tana yarinya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *