Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Daina Haifar Da Tashe-Tashen Hankula A Sassan Duniya

[ad_1]

Da yammacin jiya Talata, a yayin taron tattaunawa kan rikicin dake tsakanin kasar Rasha da kasar Ukraine na kwamitin sulhu na MDD, wakilin kasar Amurka ya yi jawabi, inda ya bata sunan kasar Sin. Shi ya sa, wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya yi watsi da tsokacin da wakilin Amurka ya yi.

Fu Cong ya jaddada cewa, cikin dogon lokacin da ya gabata, sau da dama, kasar Amurka ta bata sunan kasar Sin bisa karya da hujja mara tushe balle makama, domin kawo sabani a tsakanin bangarori daban daban, da kuma haddasa rikice-rikice. Shi ya sa, kasar Sin ta sake sa kaimi ga kasar Amurka da ta daina ture nauyin dake wuyanta, ta kuma daina haifar da tashe-tashen hankula da rikice-rikice a sassan duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *