’Yan sanda sun musanta rahotannin sace Kiristoci 170 a Kaduna

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta musanta rahotannin da ke cewa an sace wasu mabiya addinin Kirista aƙalla 163 a yankin ƙaramar hukumar Kajuru.

RFI ya ruwaito Kwamishinan ’yan sandan Kaduna, Muhammadu Rabi’u yana ƙaryata rahotannin a yayin wata ganawa da manema labarai, bayan kammala taron da suka saba gudanarwa kan tsaro.

CP Muhammad Rabi’u ya ƙalubalanci duk wanda yake iƙirarin sace mutanen da ya gabatar da hujja gami da jerin saunayen waɗanda aka sacen.

Yayin da yake nasa tsokaci kan lamarin, shugaban ƙaramar hukumar ta Kajuru, Dauda Madaki, ya ce jita-jita ce aka yaɗa amma ba wani abu ba ne face ƙanzon kurege.

A cewarsa, ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa Kurmin Wali, yankin da aka yi iƙirarin a nan ne aka sace mutanen sama da 160, amma sai suka iske cewar labarin na ƙarya ne.

Da yammacin ranar wannan Litinin wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito labarin sace ɗimbin mutanen daga kamfanin dillancin labarai na AFP, wanda ya ce gungun ‘yan ta’adda sun yi awon gaba da aƙalla mutane 163 mabiya addinin Kirista, bayan da suka afka wa wasu Mujami’u biyu a Jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya

Kamfanin dillancin labaran na AFP, ya ci gaba da cewa, shugaban ƙungiyar Kiristocin Najeriya reshen arewacin ƙasar, Rabaran Joseph Hayab, ya shaida masa cewar, daga labarin da suka samu ’yan ta’addan sun kai harin ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka tasa ƙeyar masu bautar cikin daji.

A cewar AFP, Hayab ya ce da fari mutane 172 ’yan ta’addan suka sace, amma daga bisani 9 suka tsere.

A baya dai rahotanni sun ce adadi mai yawa na ‘yan bindigar sun farwa Majami’un biyu ne inda suka yi musu ƙawanya kafin daga bisani su sace mutanen.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gano a yau Litinin ya nuna cewa an sace mutanen da yawansu ya haura 100 a jihar ta Kaduna.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *