Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 33 A Kebbi
[ad_1]
Rundunar ’Yansandan Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 33 sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Gundumar Bui, ƙaramar hukumar Arewa ta jihar. Kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi.
A cewarsa, harin ya faru ne ranar Laraba lokacin da wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka mamaye yankin da nufin satar shanu. Binciken farko ya nuna cewa maharan sun shigo ne daga Ƙaramar Hukumar Gudu ta Jihar Sokoto. Mazauna ƙauyukan Mamunu, da Awasaka, da Tungan Tsoho, da Makangara, da Kanzo, da Gorun Naidal da Dan Mai Ago sun yi ƙoƙarin kare kansu, inda a rikicin da ya biyo baya aka rasa rayuka 33.
- Jami’ar Kebbi Ta Karrama Gwamna Lawal da Digirin Girmamawa, Ta Yaba Da Ayyukan Raya Zamfara
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 2, Sun Ceto Mutane 62 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi Da Zamfara
Rundunar ’yansandan ta ce tayi haɗin gwuiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro sun ƙarfafa tsaro a yankunan da abin ya shafa. An tura ƙarin jami’ai da kayan aiki, tare da ci gaba da sintiri domin dawo da zaman lafiya da hana sake aukuwar irin wannan hari.
’Yansandan sun jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Arewa baki ɗaya, tare da gargaɗin jama’a da kada su tunkari ’yan bindiga kai tsaye saboda haɗarin da hakan ke tattare da shi. Sun kuma buƙaci a rika bayar da rahoton duk wani motsi mai sosa rai ta hanyoyin tsaro da aka tanada, yayin da ake ci gaba da farautar waɗanda suka aikata harin.
[ad_2]
Source link