An shiga fargaba bayan harin Amurka a Kwara
[ad_1]
Al’ummar garin Offa a Jihar Kwara, sun shiga fargaba a daren ranar Alhamis bayan Amurka ta ƙaddamar da hare-hare a garin.
Shaidu sun ce sun an harba wasu bama-bamai cikin dare, inda suka lalata wasu gidaje da shaguna a yankunan Yidi da Adeleke.
Wannan ya jefa mazauna yankin cikin tsoro da fargaba a ƙauye.
Zuwa yanzu dai babu rahoton rasuwar wani a hukumance.
Daga baya an gano wasu abubuwa da ake zargin bama-bamai ne da ba su fashe ba, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’ar yankin.
Wasu mazauna yankin sun danganta lamarin da ayyukan jiragen yaƙi marasa matuƙa da ƙasar Amurka ta harbo zuwa Najeriya.
A ranar Alhamis, gwamnatocin Amurka da Najeriya sun tabbatar da kai hari ta jirage marasa matuƙa a Jihar Sakkwato kan wata maɓoyar ’yan ta’addan ISIS, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaron Najeriya.
Da ta ke magana kan lamarin Offa, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kwara, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce ana ci gaba da bincike domin gano ainahin fashewar abubuwan.
Wani mazaunin gari kuma tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Tsaro, Alhaji Tajudeen Alabi, ya ce harin ya faru ne sakamakon yarjejeniyar tsakanin Najeriya da Amurka.
A cewarsa, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare, inda ya shafi kusan yankuna biyar a Offa, lamarin da ya jefa garin cikin fargaba.
Ya ƙara da cewa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kai ziyara wajen
An tura jami’an tsaro, ciki har da sojoji, zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link