Hatsarin mota ya kashe mutane 11 a Jigawa
[ad_1]
Mutane 11 sun sun rasa rayukansu yayin da wasu 12 suka samu raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar Alhamis a kan hanyar Ringim zuwa Sankara da Beguwa a Jihar Jigawa.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) da ke ƙaramar hukumar Ringin, CRC Ado Adamu ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
CRC Ado Adamu ya ce, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, wanda ya shafi wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai lambar rajista ND 983 XA, ɗauke da fasinjoji kimanin 23.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudu fiye da kima, wanda ya haifar da fashewar taya da ya faru wadda hakan ya haddasa rasa rayukan kimanin mutane 11 yayin da mutane 12 suka samu raunuka,” in ji Adamu.
Ya ƙara da cewa, an garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Ringim, inda ma’aikatan lafiya suka tabbatar da mutuwar mutane 11, yayin da waɗanda suka jikkata ke karɓar magani a halin yanzu.
Kwamandan Sashen hukumar FRSC na Jihar Jigawa, CC Umar Masa’udu Matazu, ya yi wa iyalan mamatan ta’aziyya tare da addu’ar Allah Ya jikan su.
Ya buƙaci masu ababen hawa da su bi dokokin zirga-zirga domin rage haɗurra, raunuka da mace-mace a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link