Za mu rufe Mahautar Akwanga —Gwamnatin Nasarawa
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi barazanar rufe Mahautar Akwanga saboda matsalar rashin tsafta.
Kwamishinar Muhalli da Albarkatu ta jihar, Magret Elayo, ce ta bayyana hakan a yayin ziyar da ta kai mahautar, bisa wakilcin Babban Sakataren ma’aikatar, Husseini Babayayi.
Elayo ta nuna damuwa kan yadda ake gudanar da ayyuka a mahautar cikin rashin tsafta, lamarin da ta ce yana barazana ga lafiyar al’umma.
“Wurin ba shi da tsafta, kuma yana shafar lafiyar al’ummarmu. Gwamnati za ta ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuwar al’ummarmu a Akwanga saboda yanayin wurin bai dace ba da yankan dabbobi,” in ji ta.
Ta ce idan ba a gyara ba nan da wata guda, to gwamnati ba za ta yi wata-wata ba wajen rufe mahautar gaba ɗaya.
Kwamishinar ta ƙara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da sa ido kan ayyukan mahautar har zuwa ƙarshen watan Oktoba domin tabbatar da bin ƙa’idojin tsafta.
A wani labarin kuma, an cafke mutane 112 a ƙananan hukumomi biyar na kudancin jihar saboda karya dokar tsaftar muhalli.
Babban Lauyan Hukumar Tsafta, Abubakar Mohammed, ya tabbatar da hakan, inda ya ce an kama su ne yayin aikin tsaftar muhalli na wata-wata a Lafiya da kewaye.
Ya ce an kama mutane 26 a Ƙaranar Hukumar Lafiya da wasu 26 a Keana, 21 a Awe da 21 a Obi, sai kuma 18 a Doma.
An gurfanar da su a gaban kotun tafi-da-gidanka, inda aka hukunta su gwargwadon laifin da kowanne ya aikata.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link