Yadda Azumi Yake Sa Tsoron Allah
[ad_1]
Kamar yadda muka yi bayani a baya, azumin watan Ramadana wajibi ne ga dukkan Musulmi baligi mai lafiya, ba mara lafiya ba. Wajibcin azumi kamar yadda Allah ya fada a cikin Alƙur’ani da fadarsa yana cewa:
“Ya ku Muminai, Allah Ya wajabta muku yin azumi kamar yadda Ya wajabta ma waɗanda suka zo kafin ku, ko za ku ji tsoron Ubangijinku. Kwanaki ne ƙididdigaggu. Wanda ya kasance a cikinku bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya rama abin da ya kubuce masa a wasu ranakun. Waɗanda kuma ba za su iya yin azumin ba, to su ciyar da miskinai. Amma wanda yake da damar ciyar da miskinai da yawa, to ya yi alkhairi ne a wajensa. Lallai yin azumin ya fi alkhairi a gare ku, idan kun san alkhairin da ke cikinsa.
Lallai watan Ramadana da aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane, sannan kuma akwai ayoyi bayyanannu a cikinsa masu shiryarwa zuwa ga Allah da bayyana hukunce-hukunce. Duk wanda ya halarci ganin watan, to ya azumce shi. Wanda kuma bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya biya abin da ya tsere masa a sauran wasu ranakun. Allah sauƙi yake nema daga wurinku, ba wahalarwa ba. Allah yana son ku cika adadin azumin, sannan yana son ku yi masa kirari daga abin da Ya shiryar da ku, ko za ku gode masa?”
Yana daga cikin falalar azumi cewa yana sa tsoron Allah, saboda yana karya sha’awa. Yana daga cikin fa’idar azumi, Allah ya ce don mu yi takawa. Takawa mataki-mataki ce: akwai ta gama-gari, da ta kebantattu, da ta kebantattun kebantattu.
Takawa ta gama-gari: ita ce a bar ci da sha har izuwa faɗuwar rana, sannan a yi aiki don neman lada, a kuma bar abin da bai dace ba. Wannan takawar ba ta hana wasu yin abin da bai dace ba.
Takawa ta kebantattu: ita ce a bar ci da sha har izuwa faɗuwar rana, a yi ayyuka don Allah, sannan ba za su yi ƙarya ba, ba za su yi husuma ba, ba za su yi cece-kuce ba. Za su shiga cikin ibada ta ko’ina.
Takawa ta kebantattun kebantattu: sun haɗa duk abin alkhairi na gama-gari, sun haɗa duk abin alkhairi na kebantattu, sannan sun ƙara da nutso da zurfafawa cikin sanin Allah. Ba su ganin wani sai Allah; a ko da yaushe suna fadar Allah ko fadar Annabi (SAW) ko fadar waliyyan Allah.
Waɗannan takawa guda uku, Allah ya faɗa mana su cikin Alƙur’ani yana cewa:
“Ba laifi ga waɗanda suka yi imani da Allah suka yi aiki mai kyau cikin abin da suka ci, idan suka yi takawa suka yi imani, sannan suka yi wata takawa kuma suka yi imani, sannan suka yi wata takawa sannan suka yi kyautaye.”
Ayar ta sauka ne lokacin da ayar haramta giya ta sauka, sai wasu daga cikin muminai suka shiga shakku suna cewa: “To yanzun ‘yan uwanmu muminai da suka sha giya a baya kuma suka mutu fa?” Sai Allah ya saukar da wannan ayar yana mai cewa ba laifi a gare su, domin sun mutu lokacin da ba a haramta giya ba.
Alhamdulillah, duk waɗannan takawa guda uku suna daga cikin falalar Ramadana: takawa cikin Musulunci, takawa cikin Imani, sai takawa cikin Ihsani.
Azumin Ramadana kwanaki ne ƙididdigaggu, wata ɗaya ne kacal cikin watanni sha biyu. Allah ya bayyana mana cewa Ya san akwai marasa lafiya a cikinmu kuma akwai matafiya, don haka su ƙididdige kwanakin da azumi ya tsere musu su rama a wasu kwanakin.
Ayar da ta gabata ta bayyana wajibcin azumin watan Ramadana a Alƙur’ani, sai kuma hadisi mai zuwa ya tabbatar da wajibcin azumin a Sunnah ta Annabi (SAW):
“An gina Musulunci a kan shika-shikai guda biyar:
Shaidawa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne.
Tsayar da sallah.
Ba da zakka.
Azumin watan Ramadana.
Ziyartar Dakin Allah mai girma.”
Ya zo a cikin hadisin Dalhatu bin Abdullahi cewa wani mutum ya tambayi Annabi (SAW): “Ya Manzon Allah, gaya min abin da Allah ya wajabta min na azumi.” Sai Annabi ya ce: “Watan Ramadana.” Sai mutumin ya ce: “Akwai wani kuma?” Sai Annabi ya ce: “A’a, sai dai idan za ka yi na nafila.”
Babu jayayya a cikin al’ummar Musulmi kan wajibcin azumin watan Ramadana.
An wajabta azumin watan Ramadana ranar Litinin, bayan hijira shekara ta biyu. Bayan Annabi (SAW) ya yi hijira zuwa Madina, a cikin shekara ta biyu ne aka wajabta azumi.
Alhamdulillah, abin da ya gabata shi ne bayanin azumi daga littafin Allah, da Sunnah ta Annabi Muhammad (SAW), da kuma haɗin kan al’ummar Musulmi kan wajibcin azumi.
Nasa’i ya ruwaito daga Abi Umamata cewa ya ce: “Ya Manzon Allah, horar da ni da wani aiki.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Na hore ka da yin azumi, bayan farillah ka dinga yin nafila, domin azumi ba shi da kama cikin ibada.” Domin kowace ibada riya na iya shiga, amma azumi ba haka ba ne.
Wannan ya nuna alaƙar Ubangiji da azumi, domin Ubangiji ba shi da misali kamar yadda azumi ma ba shi da misali.
Muslim ya ruwaito daga Abi Huraira cewa Manzon Allah (SAW) ya ce:
“Ubangiji Ya ce dukkan ibadar ɗan Adam tasa ce, sai dai azumi nawa ne, kuma ni ne zan saka masa.”
Ya zo cikin hadisi cewa:
“Azumi garkuwa ne. Idan ɗayanku yana azumi, kada ya faɗi magana mara kyau, kada ya yi hayaniya. Idan wani ya zage shi ko ya nemi husuma da shi, ya ce ni mai azumi ne. Na rantse da wanda ran Annabi Muhammad (SAW) ke hannunsa, warin bakin mai azumi ya fi ƙamshi a wurin Allah ranar lahira fiye da turaren almiski.”
Muslim ya ruwaito daga Sa’adu cewa Manzon Allah (SAW) ya ce:
“A cikin Aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, ba masu shiga ta sai masu azumi.”
Mu sani ya ku ‘yan uwa, Allah Ya amsa mana azumin Ramadana. Ma’anar azumi ita ce kamewa. Azumi ibada ce da babu misalinta kamar yadda Ubangiji ba shi da misali. Kowace ibada ana cewa “na yi” — na yi sallah, na yi zakka amma azumi ana cewa “na bari” na bar ci, na bar sha, na bar saduwa da iyali.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah.
Godiya ga Allah.
[ad_2]
Source link