A Bangaren Kyawawan Dabi’u, Annabi SAW Ma’aiki Ne Ga Duk Halitta
[ad_1]
Annabi SAW, gwarzon namiji ne wanda duk halitta babu kamarsa. Annabawa su ne gaba-gaba a halittar Ubangiji ta bangaren wayewa, halittar jiki, tausayi da tsiratar da dan Adam, da kuma girmama Ubangiji. Annabi Muhammad SAW, shi ya cika dukkan Annabawa kuma ba a cika abu sai da wanda ya fi duk sauran da suka gabata.
Manzon Allah SAW, gwarzon dan Adam ne, cikakke wanda ya kawo wa duniya juyi da ci gaba ta hanyar addini da siyasa – shiryawa dan Adam yadda zai yi mu’amala mai kyau da sauran ‘yan Adam duk irin yadda duniya ta sauya.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 22, Sun Ƙwato Makamai, Motoci, Da Ƙwayoyi A Faɗin Nijeriya
- Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno
A bisa al’adar dan Adam, duk wanda ya kawo masa sauyi na alkairi a rayuwarsa, za ka samu yana girmama wannan, har ya riki wata rana ta musamman don nuna murna ga wannan da ya kawo masa wannan sauyin na alkairi a rayuwarsa. Misali, Annabi SAW da ya kawo mana addini kuma ya wayar da mu. Nuna irin wannan murna, al’ada ce ta dan Adam. Don haka, a matsayinmu na ‘ya’yan Adam, muke taruwa duk shekara, muna murna da samun wannan fiyayyen shugaba, Annabi Muhammad SAW.
Annabi SAW, an haife shi a Makka, babban gari inda dakin Allah (Ka’aba) yake. An saka masa suna Muhammadu (shayabon halitta), Annabawa sun fi sanin shi da Ahmadu (mafi tsantsar godiyar Allah). Mahaifin shi Abdullahi dan Abdulmudallib, dan Hashim… har zuwa Adnan, kakanni kusan 37 daga Adnan zuwa Annabi Ibrahim AS. Mahaifiyarsa, Aminatu binti Wahbi (Shugaban bani Zuhrata). An haifi Annabi SAW a 20 ga watan Afrilu 571 bayan haihuwar Annabi Isah (AS). Allah ya aiko Annabi SAW a 10 ga watan Agusta, 610, ya yi Hijira 23 Satumba, 622, ya yi nasara a kan harin Kuraishawa a Badr a 23 Maris, 623. Ya kama garin Makkah a bisa umarnin Ubangijinsa don ya tsarkake ta a 10 ga watan Janairun 630, ya yi hajjin bankwana, inda ya yi wa al’ummarsa wasiyyar duk abin da ya dace da ita, wanda anan ne ayar “Alyauma akmaltu lakum dinakum, wa’atmamtu alaikum ni’imati, waraditu lakumul ISLAM dina – yau na cika muku addininku, na cika ni’imata a gareku, kuma na amince muku, MUSULUNCI ya zama addininku) ta sauka. Addinin da ya fara, tun daga Annabi Adam AS, yau an cika shi da Annabi Muhammad SAW.
Wannan addini, shi ne addinin Musulunci wanda ya fara tun daga Annabi Nuhu AS. Duk Annabawa, cewa, suke su Musulmai ne, kai har da Aljannu, da fadinsu, “wa’anna minnal MUSLIMUNA wa minnal kasidun”; Annabi Ibrahim, “makana Ibrahimu Yahudiyya wala Nasraniyyan, walakin kana hanifan MUSLIMA”; Annabi Yakub, “Wa ausa biha Ibrahimu banihi Wa Yakub, ya baniyya innallahasdafa lakummuddina fala tamutunna illa wa’antum MUSLIMUN”; Annabi Yusuf, “rabbi kad ataitani minal mulki wa allamtani min ta’awilil ahadis, fadirassamawati wal’ardi, anta waliyyi fiddunya wal akira, tawaffani MUSLIMAN wa alhikni bissalihin”; Annabi Musa, “ya kaumi in kuntum amantum billahi, fa alaihi tawakkalu in kuntum MUSLIMIN”; ‘Yan sihirin Fir’auna, “Wama tankimu minna illa an amanna bi’ayati rabbina lamma ja’atna, rabbana afrig alaina sabran wata waffana MUSLIMIN”; Fir’auna, “wajawazna bibani Isra’ilal bahra fa’atba’ahum fir’aunu wa junuduhu bagyan wa’adwa, hatta iza adrakahul garaku, kala amantu annahu la’ilaha illallazi amanat bihi banu isra’ila wa ana minal MUSLIMIN.” kuma Ubangiji bai ce karya yake ba, sai dai ya ce, amma “wa’anta minal mufsidin – kana cikin masu ɓarna” saboda Musulmi zai iya zama mai laifi. Annabi isa da mabiyansa, “Falamma a hassa isa min humul kufra kala man ansari ilallah, kalal hawariyyun nahnu ansarullah, amanna billahi wash had bi’anna MUSLIMUN”; Annabi Nuhu, “fa,in tawallau fama sa’altukum alaihi min ajri, in ajriya illa alallah, wa umirtu an akuna minal MUSLIMIN”; Annabi Sulaiman da sarauniya Bilkisu, “Alla ta’alu alayya wa’atuni MUSLIMIN. Wa ASLAMTU ma’a sulaiman lillahi rabbil alamin”; sauran Annabawa duka, “inna anzalnat taurata fiha hudan wa nur, yahkumu bihan nabiyyunallazina ASLAMU”; Annabi SAW da al’ummarsa, “Kul inna salati, wa nusuki wa mahyaya wa mamati lillahi rabbil alamin, la sharikalah, wa bizalika umirtu wa’ana awwalul MUSLIMIN”.
Annabi Muhammad SAW, ya koma ga Ubangijinsa, a ranar 8 ga watan Yunin 632.
Manzon Allah SAW da duk alkairan da Allah ya ba shi, ya tattare su acikin abu Uku:
1 – kasanacewarsa an turo shi ne ga dukkan mutane, “Kul ya ayyuhannasu inni Rasulullahi ilaikum jami’an… – ka ce, ya ku mutane, lallai ni Manzo ne zuwa gare ku baki daya”. Amma inda masu tafsiri ke rikitawa shi ne, in an ce, “ya ayyuhannasu” sai su ce, “ya ahla Makkata” bayan kuma Annabi SAW na duk duniya ne ba Larabawa kadai ba – Rumawa, Yahudawa, Farisawa, Sinawa, Turawa, Afirka, Amurkawa,…
Don haka, Allah ya ce, “ya ayyuhannasu inna kalaknakum min zakarin wa unsa, wa ja’alnakum shu’uban wa kaba’ila lita’arafu – ya ku mutane, mu muka halicce ku dangin namiji da mace, kuma muka sanya ku zama ‘yan kasashe mabambantan harsuna, don ku iya banbance kawunanku”
Tun da Annabi SAW ma’aiki ne ga duk dan Adam, to ba ma’aiki ne mai halin Larabawa kadai ba, ba ma’aiki ne mai halin Afirka ba kadai ko wani yanki, a’a, ma’aiki ne mai halin duk ‘yan Adam – kyawawan dabi’u, tausayin dan Adam da girmama Ubangiji.
Manzon Allah SAW ya zo da kyawawan dabi’u, wanda sune tafarki madaidaici wanda ya dace da duk halitta. In kana da kyawawan dabi’u, duk inda ka shiga a duniya, za a karbe ka, musamman yankin Turawa, da kyawawan dabi’u suka yi fice. Da yawan masu wa’azi ba su cika bai wa wannan ɓangare karfi ba, sai dai wa’azi akan Annabi SAW a al’adar Hausawa ko kuma Larabawa. Da kyakkyawar dabi’a ya dace a yi kira.
Annabi Musa AS, Ubangiji ya saukake masa shari’ar Hamurabi ta Sarkin Babila (wata kila Annabi ne), wacce ta ke dauke da hukuncin kisa 24 amma Annabi Musa ya zo da 12, da Annabi Isa AS ya zo, shi kuma sai ya zubar da kisan gaba daya, ya dauki kyawawan dabi’u da ake kira, wasayal Ashri (10) ta Annabi Musa, ta zamar masa hikima. Wannan wasayal ashri, mu ma al’ummar Annabi Muhammad SAW, Allah ya tabbatar mana da ita acikin Alkur’ani, sabida su din, addinin duk halitta ne, babu wata Masarauta ko fadar gwamnati da za ta guji wannan dabi’un. Ga su kamar haka:
– kar ku hada Allah da wani
– ku girmama Iyaye
– kar ku kashe ‘ya’yanku don tsoron talauci, Allah ne zai azurta ku da su.
– kar ku kusanci Alfasha (Auren jinsi daya, ko auren wanda Allah ya haramta mana)
– kar ku kashe rai sai wacce aka halasta. DOKA MAI KARFI, A KULA DA ITA, a shari’a, bangaren ciyayya da shaye-shaye – komai Halal ne sai abinda shari’a ta haramta amma a bangaren daukar rai, akasin haka ne, ma’ana, komai haram ne sai abin da shari’a ta halasta.
– kar ku kusanci dukiyar maraya sai don ta karu
– ku cika ma’auni – sikeli, mudu, da duk wani nau’in awo.
– idan za ku yi magana, ku fadi gaskiya
– ku cika alkawari tsakaninku da Ubangijinku
– ku tsaya kan wannan kyawawan dabi’un da aka zayyano.
A bangaren kyawawan dabi’un da muka zayyanu, Annabi SAW, ma’aiki ne ga duk halitta.
… za mu ci gaba a mako mai zuwa.
[ad_2]
Source link