Amurka Ta Bayyana Dalilin Janye Jakadanta Daga Nijeriya Da Wasu Kasashe 29

[ad_1]

Shugaba Donald Trump, ya janye jakadan Amurka na Nijeriya, Richard M. Mills Jr., da na wasu manyan kasashe 29 na duniya.

Ambasada Mills, wanda aka nada a ranar 25 ga Yuli, 2024, yana cikin jakadu 13 da ke aiki a kasashen Afirka, wanda masu sharhi a Washington suka ce; hakan na nufin sake fasalin manufofin harkokin wajen Amurka a kan ajandar Trump.

  • Sheikh Al-Sudais Ya Gargadi Masu Ibadah Kan Kiyaye Darajar Masallatan Harami
  • An Yi Bikin Murnar Cika Shekaru 15 Da Kafuwar Asibitin Abota Na Sin Da Ghana

A cewar kamfanin dillancin labarai na AP, jami’an diflomasiyyar da abin ya shafa, wadanda aka nada, da yawa daga cikinsu an nada su ne a lokacin gwamnatin Biden, amma sai suka ci gaba da rike mukamansu tun a farkon watannin Trump a ofis, an sanar da su a makon da ya gabata cewa; wa’adinsu zai kare a watan Janairun 2026.

Wani jami’in da ke da masaniya kan ci gaban ya shaida wa AP cewa, “Jakadan suna aiki ne bisa yardar shugaban kasa, duk da cewa; yawancisu suna kan mukaminsu na tsawon shekaru uku zuwa hudu.”

Jami’an, wadanda suka bukaci a sakaya sunansu, sun bayyana cewa; ba korar jakadun aka yi daga ma’aikatar harkokin wajen ba, za a mayar da su Washington ne, domin wasu ayyukan daban idan sun zabi ci gaba da aikin nasu.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ta ki tabbatar da adadin wakilan da abin ya shafa, amma ta kare matakin, tana mai bayyana shi a matsayin “daidaitaccen tsari a kowace gwamnati.”

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce, “Jakada wakilin shugaban kasa ne, kuma hakkin shugaban kasa ne tabbatar da cewa; yana da mutane a kasashe wadanda kare muradu da ajandar Amurka ita ce farko.”

Afirka ita ce yankin da aka fi fama da matsalar, inda aka kira jakadu daga kasashe 13: Burundi, Kamaru, Cape Berde, Gabon, Cote d’Iboire, Madagascar, Mauritius, Nijar, Nijeriya, Rwanda, Senegal, Somalia da kuma Uganda.

Yankin Asiya zuwa Pacific ya biyo bayan sauye-sauye na jakadanci shida a Fiji, Laos, Tsibirin Marshall, Papua New Guinea, Philippines, da Bietnam. Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da jakadu a kasashen Turai hudu (Armenia, Macedonia, Montenegro, da Slobakia), biyu a Gabas ta Tsakiya (Algeria da Masar), biyu a Kudancin Asiya (Nepal da Sri Lanka), da biyu a Yammacin Duniya (Guatemala da Suriname).

Janye jakadun, ya yi nuni da daya daga cikin manyan sauye-sauyen diflomasiyya a karkashin wa’adin Trump na biyu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *