Jiragen soji sun yi raga-raga da cibiyoyin Boko Haram a Borno

[ad_1]



Jiragen Rundumar Sojin Sama ta Najeriya sun kashe mayaka da dama bayan sun yi ruwan bama-bamai a kan sansanoni da ma’ajiyar makaman ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a yankin Dabar Masara da ke Kudancin Tumbuns na Karamar Hukumar Monguno a Jihar Borno.

Rundunar ta ce an kai wannan harin ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Disamba, 2025, bayan samun sahihan bayanan sirri cewa wuraren na zama cibiyar horarwa da rarraba kayayyakin yaki ga ’yan ta’adda a wannan yankin.

Majiyar ta ce, binciken leken asiri kafin kai harin ya gano motocin ’yan ta’adda da aka boye karkashin ciyayi, tare da yawan karar harbin makamai a yankin, lamarin da ya tabbatar da muhimmancin wurin a ayyukan ’yan ta’addan.

Rahoton ya ce, kafin kai harin, sai da aka sake tabbatar da dukkan bayanan kafin a kaddamar da farmakin bisa ka’idojin aikin soja.

Haka nan bayan kai harin, rahoton tantance barnar ya nuna cewa an lalata motocin ’yan ta’adda tare da kashe da dama daga cikinsu.

Rundunar ta ce wannan nasara na nuna jajircewarta wajen amfani da sahihan bayanan sirri da hare-haren da aka tsara domin murkushe cibiyoyin ’yan ta’adda a yankin da ma ilahirin shiyyar Arewa maso Gabas.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *