APC ta lashe duk kujerun zaben Ƙananan hukumomin Borno
Sakamakon zaben shugabanni da kansiloli na ƙananan hukumomin Jihar Borno da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar ta gudanar a ranar Asabar ya nuna cewa Jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta lashe dukkan kujerun shugabanni na ƙananan hukumomi 27 da kuma kujerun kansiloli 312 a faɗin jihar.
Shugaban hukumar zaben jihar, Dakta Tahiru Shettima, ya bayyana wa manema labarai a ofishin hukumar da ke Maiduguri da yammacin Lahadi cewa Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe dukkan kujerun shugabanni da na kansiloli a jihar.
A cewarsa, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da adalci, abin da ya tabbatar da cewa hukumar ta cika alƙawarin da ta ɗauka tun farko na gudanar da gaskiya da rikon amana.
Zaben da aka gudanar ya samu halartar jam’iyyun siyasa kusan shida, sai dai daga baya Jam’iyyar PDP ta janye daga fafatawar bisa zargin cewa ba za a yi mata adalci ba.
Wani jigo daga Jam’iyyar Labour, wanda ya nemi a sakaye sunansa saboda dalilan siyasa, ya bayyana cewa su a matsayinsu na ‘yan adawa sun gamsu ƙwarai da sakamakon da aka samu.
A nasa bangaren, wani ɗan jam’iyyar APC a Maiduguri, Malam Qauwami Aji, ya ce: “Ni ma ban taɓa shakkar za mu fadi ko da kujera ɗaya ba. Tunda hukumar mu ce ta gudanar da zaben, to yaya za mu fadi?”
Shi kuwa Umara Babagana, mazaunin Maiduguri daga Jam’iyyar NNPP, ya ce: “Ai dama mun san abin da za a yi. Mu ’yan adawa mun san tuwo na maina Jam’iyyar APC za ta yi mana. Allah ya kyauta.”