’Yan sanda sun tura motocin sulke 13 zuwa Kebbi

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kebbi ta karɓi motocin sulke guda 13, da sauran motocin aiki daga Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kebbi, Bello M. Sani, ya mika motocin ga Gwamna Nasir Idris a Fadar Gwamnatin Jihar a ranar Litinin.

Ya ce: “Sufeto-Janar ya ga dacewar ƙarfafa ƙoƙarinku wajen shawo kan matsalolin tsaro a jihar ta hanyar samar da ƙarin motocin sulke da sauran motocin aiki domin ƙara nasarorin da aka samu.”

Ya ƙara da cewa wannan ƙarfafawa na nufin inganta tasirin ayyukan rundunar, faɗaɗa sintiri, da kuma tallafawa gaggawar amsa matsalolin tsaro a faɗin jihar.

Kwamishinan ya jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar wa jama’a cewa za a yi amfani da sabbin kayan aikin cikin tsari domin ƙarfafa tsaro a dukkan sassan jihar.

Gwamna Idris ya yaba wa Sufeto Janar na ’Yan Sanda da Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi bisa ƙoƙarinsu na ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da yin haɗin gwiwa da ‘Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro domin shawo kan ayyukan laifi a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *