Sojojin Najeriya da Burkina Faso ta tsare na neman ɗauki
[ad_1]
Jami’an Rundunar Sojin Sama ta Najeriya 11 da aka tsare jirginsu a ƙasar Burkina Faso, sun roƙi gwamnatin Najeriya ta yi gaggawar kawo musu ɗauki.
Sojojin da suka yi magana ta hannun wasu abokansu, sun bayyana cewa ci gaba da tsare su ya zama tamkar garkuwa.
“Mai yiwuwa su yi bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara a tsare a ƙasar waje,” in ji wani abokinsu.
Ƙasar Burkina Faso na ci gaba da tsare jami’an sojin saman Najeriya 11 tun bayan da jirginsu ya sauka a ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta sanar a ranar Litinin cewa ana tsare da sojojin ne bayan jirginsu na jigilar kaya ƙirar C-130 ya sauka a garin Bobo-Dioulasso makon jiya.
Hukumomin Burkina Faso sun zargi tawagar da karya dokokin sararin samaniya tare da iƙirarin cewa sun tilasta wa jirgin sauka ne.
Amma Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta musanta zargin, suna masu cewa jirgin ya karkata zuwa Burkina Faso ne saboda matsalar na’ura da ya samu a hanyarsa ta zuwa ƙasar Portugal domin gyaran lokaci-lokaci da aka tsara.
Majiyoyin Rundunar Sojin sun yi watsi da raɗe-raɗin leƙen asiri ko ayyukan boye, suna jaddada cewa jirgin na tafiya ne na yau da kullum kuma yana da dukkan takardun izini na ƙasa da ƙasa.
“Ba kama jirgin aka yi ba, ba a tilasta shi sauka ba, kuma ba a taɓa samun shi yana aiki ba tare da izini ba,” in ji wata majiya.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar cewa jami’an ba a sako su ba, ya kuma ce an hana Jakadan riƙon ƙwarya na Najeriya ganin su a lokacin da ya kai ziyara makon jiya. Ya ƙara da cewa ana ci gaba da tattaunawa da hukumomin Burkina Faso domin a sako su kafin Kirsimeti.
“Ma’aikatar na gudanar da muhimman tattaunawa da hukumomin Burkina Faso. Ba daidai ba ne a ce ba mu yin komai,” in ji Ebienfa.
Lamarin ya haifar da raɗe-raɗi a intanet, amma jami’an Najeriya sun roƙi jama’a su yi watsi da iƙirarin leƙen asiri ko tallafin waje, suna masu cewa labaran ƙarya ne da aka ƙirƙira domin tayar da hankali da kuma lalata dangantakar yankin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link