Batun Kudurin ‘Yan Majalisar Amurka Kan Kwankwaso Da Fulani Makiyaya

[ad_1]

‘Yan Majalisar kasar Amurka na jam’iyyar Republican, a ranar 11 ga watan Fabirairun  2026, sun gabatar da wani kuduri kan bukatar, a kakabawa tsohon gwaman jihar Kano Dakta Rabiu Kwankwaso da kuma wani sashe, na ‘yan kabliyar Fulani, da ‘yan majalisar, suka yi ikiran cewa, ‘yan ta’adda ne, takunkumi.

Sun gabatar da wannan kudurin na su ne dai, bisa kafa hujjarsu kan zargin sarkakiyar yin amfani da addini wajen yin hukunci da kuma tauye hakkin bill adama, musamman a Arewacin kasar nan.

  • Makomar Nijeriya Na Hannun FIFA – Shehu Dikko
  • Jerin Sharuddan Da Chelle Ya Gindayawa NFF Domin Cigaba Da Jagorantar Super Eagles

Kudurin na su, ya kuma bukaci da a  wanzar da dokar bayar da damar ‘yancin gudanar da addini, ba tare da wata tsangwama ba, inda kuma, suka bukaci da a kakabawa kadarorin Kwakwaso da kuma soke katin bizarsa.

Duba da cewa, wannan kudurin na ‘yan majalisar, ya kasance tamkar wani yinkuri ne, na tauye ‘yancin marasa karfi, hakan ya Dabo ya  kuma haifar da mummunar ce-ce kuce, a Bangaren huddar difolomasiyya ta kasa da kasa, tare da kuma bijero da tambayoyi, kan yin katsalandan daga ketare, kan lamarin da ya shafi kasar nan.

Wannan Jaridar ta yi nazari kan illolin da ke tattare da wannan kudurin na’yan majalisar, musamman ganin cewa, kudurin, ya karkata ne, kan wani Bangaren daya kawai wanda hakan ya kuma nuna cewa, ana bukatar sauye-sauye ne kawai na cikin gida, ba wai hasashen ‘yan bani na iya, daga ketare ba.

Kazalika, wannan kudurin, bai da wata nasaba da karancin ci gaba da tashen da Kwankwaso ke ci gaba da samu, a fagen siyasar jiharsa ta Kano ba ne ko kuma yawan sukar wasu tsare-tsaren gwamnatin tarayya ba ne, da kuma yadda a karkashin tafiyarsa a karkashin ta Kwankwasiyya, da ke ci gaba da kare muradun Arewacin kasar nan ba.

Masu yin sukar adawa a majalisar ta Amurka suna kawai danganta Kwankwaso, da wanzarwa da kuma ganin, an kaddamar da Shari’a Musulunci, a birnin na Dabo, inda ake yanke hukunci, kan duk wanda ya yi wani Batanci, kan Manzo Allah SAW, inda kuma aukuwar rikice-rikice, ka janyo hankalin kasashen duniya.

Bugu da kari, sanya jagororin ‘yan kabilar Fulani a cikin jeren ‘yan ta’adda, hakan ya nuna zargin da ake yiwa Fulani Makiyaya, a matsayin wadanda, ke janyo rikice-rikicen manoma da Fulani Makiyaya a kasar, amma abin takaicin, sai aka danganta hakan a matsayin, aukuwar rikice-rikicen addini.

Sai dai, za a iya  irin wadannan rikice-rikicen, sun samo asali ne daga karancin kudade da sauyin yanayi da kuma gazawar, iya gudanar da shuganci na gari a kasar.

Dangane da wasu alkaluma da aka samu daga yankunan da ake sanun aukuwar rikice-rikicen da ake yin amfani da makamai wato ACLED, sun nuna cewa, akwai hannun wasu Fulani Makiyaya, musamman kan batun kokarin samu wajen yin kiwon dabbobi fiye da batun rikicin addini.

Nijeriya dai, ta sha kin amince wa da duk wani yunkuri, na yi mata katsalandan, a cikin al’amuranta, daga ketare, musamman wanda hakan, ke kunshe, a cikin kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da aka sabunta da kuma yarjejeniyar kare ‘yancin bil’Adama ta Afirka

Kakaba takunkimi ga wasu fitatfitattun ‘yan siyasa musammna rinsu Kwankwaso za a iya cewa, wata bita da kullin siyasa, musamman duba da cewa, zaBen shugaban kasa, na 2027 na kara kunno ka.

Hakazalika, akwai kuma batun kara karfafa huddar Jakadanci, a tsakanin Nijeriya da kasar Amurka, wadda take kara neman hadin kan Nijeriya, kan dakile ta’addanci na kasa da kasa da kuma daidaita al’amura a yankin Sahel.

A Bangaren tattalin arziki kuwa, za a iya cewa, wannan kudurin na ‘yan majalisar Amurka ta kakabawa kadarorin Kwakwaso takukumi da kuma soke katin bizarsa, a namu ra’ayin hakan zai kawo cikas ga zuba jari a jihohin da ke Arewacin kasar, musamman ganin cewa, daukakar da Kwankaso yake da ita a yankin, na nan daram-dam

Birnin na Dabo dai, na ci gba da amsa sunansa, na yankin da ya yi karfi, a fagane hada-hadar kasuwanci, ba wai kawai a Kanon kadai ba, har da ketare, wanda hakan ke nuna cewa duk wani yunkuri na kawo koma bayan ci gaba da gudanar da hada-hadar kasuwanci a jihar, hakan zai kara haifar da mummunar matsin tattalin arziki, musamman duba da yadda tuni, kalubalen rashin tsaro, ya yi kamari.

A zahirance dai, wannan kudurin, ya karkata ne, kan Sharia’r Musulunci da kuma kan Fulani Makiyaya, inda hakan ke ci  gaba dora alamar tambaya, na rashin yin adalci.

Kasar nan dai, na gudanar da tsari biyu na Bangaren Shari’a wanda ake wanzar da Shari’ar kan lamaru na kasshin kai da kuma a Bangaren batutuwan da suka shafi, aikata manyan laifuka, tun a lokacin da ake da jihohi 12 a Arewacin kasar, wato tun a 2000.

Wannan tsarin dai, an samar da shi ne, tun lokacin da aka rarraba kasar a 1914 wanda ya bai wa Musulmai, damar gudanar da lamauransu, a bisa tsarin tarayya.

Kazalika, tun a lokacin da turawan mulikin mallaka, suka jagoranci kasar, musamman a lokacin Lord Lugard, mulkinsa ya bai wa Musulmai, damar tafiyar da lamauransu, kan turbar Shari’a, inda aka samar da kotunan Muslunci da ke yankewa Musulmai zalla, hukunci.

Batun na daukar doka a hannun da Musulmai ke yi, ga duk wanda ya yi Batanci kan Manzo Allah SAW, za iya cewa, hakan na faruwa ne, saboda sakacin gwamnati, na daukar matakin gaggawa ga duk wanda ya aikata wannan laifin.

Wani abinda dubi a nan shi ne, su kansu Fulani Makiyaya, ba su tsira wajen zamowa wacanda ‘yan bindiga, ke kai wa hare-hare ba, tare da kuma yadda matsalar sauyin yanayi, ke shafar rayuwarsu, har ta kai ga, ta tilasa ta su, barin matsugunan su.

Alumma da dama da Arewacin Nijeriya, kalubalen rashin tsaro, ya raba su, da rayuwarsu cikinsu har da kuma wasu mabiya addinin Kirista.

An kuma samu rahotanni da ban da ban na kai hare-hare, a guraren da ake gudanar da ibada, a saboda haka, ya zama wajibi, Nijeriya ta shi tsaye, ta tunkaro magance kalubalen rashin tsaron, da ya jima, yana addabar kasar.

Bugu da kari, dole ne gwamnatin kasar nan, ta tsaya kai da fata wajen kin amincewa, da wannan kudurin na ‘yan majalisar Amurka.

Suma gwamnonin da ke a Arewa, dole ne, su samar da wani tsarin tabbatar da tsaro, a cikin yankunan su, kmaar da irin sabon tsarin da gwamnatin Kaduna mai ci, ta kirkiro da shi, na  kara wanzar da tsaro, wanda akalla, ya rage samun aukuwar matsalar tsaro, har kusan kaso 25, a shekarun da suka wuce.

Akwai bukatar ta hanyar yin amfani da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan lamarin tsaro, a saita lamura, musamman kan lalubo da mafita, kan batun talauci da sauyin yanayi, duba da cewa, wadannan batutuwan biyu, na dga matsalar, da ke kara haddasa aukuwar rikice-rikice, a tsakanin manoma da Fulani Makiyaya.

Kazalika, ya kamata kasar ta kara karfafa huddalar diflomasiyya da Amurka da kuma kungiyar nahiyar Afirka wato AU musamman wajen samar da sauye-sauye, masu dorewa a cikin kasar nan.

Wannan barazanar ta ‘yan majalisar Amurka, da suka auna ta kan Kwankwaso da ‘yan kabilar Fulani, a namu ra’ayin hakan na nuna cewa, ‘yan bani na iya da ke a ketare, son sanya Tabarau dinsu, suna liken kalubalen da Nijeriya ke ciki.

Samun hadin kan kasar dai, ba wai ‘yan tsiraru daga ketare ne, ke da wani ikon, kakabawa wani sashen jinsi na kasar takunkumi ba, amma kamata yayi, mahukuntan kasar, su samar da sauye-sauyen da za su inganta raywar ‘yan kasar

Ta hanyar zuba jari a Bangaren tsaro, musamman a Arewacin Nijeriya da kuma  adaukacin fadin kasar, hakan zai kawar da duk wani tarnaki da kasar ke fuskanta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *