El-Rufai Ya Zargi ICPC Da DSS Kan Tsare Shi Ba Bisa Ƙa’ida Ba Da Neman Ya Yi Ritaya Daga Siyasa

[ad_1]

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da ƙara a gaban kotun majistare da ke Abuja, inda yake zargin jami’an ICPC da DSS da tsare shi ba bisa ƙa’ida ba tare da ƙoƙarin tilasta masa yin ritaya daga siyasa.

A cikin ƙarar, ya ambaci shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu, da Darakta Janar na DSS, Adeola Oluwatosin Ajayi, tare da wasu jami’ai.

  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 27
  • Harin Maiduguri: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Saƙon Trump A Kan Tinubu

El-Rufai ya ce an tsare shi tun ranar 18 ga watan Fabrairu, 2026, ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Ya bayyana cewa tun farko ya je ofishin EFCC a ranar 16 ga watan Fabrairu, inda ya bayar da bayani kuma ya haɗa kai da masu bincike, sannan aka ba da belinsa.

Sai dai ya ce jami’an DSS sun ɗauke shi daga hannun EFCC suka kai shi wajen ICPC kafin ya cika sharuɗan belinsa.

Ya kuma ce umarnin kotun da aka yi amfani da shi wajen tsare shi ba shi da inganci, kuma ya ƙare a ranar 4 ga watan Maris, 2026.

Tun daga lokacin, ya ce babu wata hujja ta doka da ta bayar da damae tsare shi.

Har ila yau, El-Rufai ya zargi jami’an ICPC cewa ba za su sake shi ba sai ya daina siyasa, abin da ya ce ya saɓa wa haƙƙoƙinsa na kundin tsarin mulki.

Ya ƙara da cewa an hana shi samun cikakkiyar damar ganin iyalansa, lauyoyinsa da likitocinsa.

A ƙarar, ya zargi jami’an da suka tsare shi ba bisa ƙa’ida ba da kuma taƙaita masa ‘yancin zirga-zirga, inda yake roƙon kotu ta ɗauki mataki.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ICPC da DSS ba su yi wata magana kan zargin ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *