An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro

[ad_1]



Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Filato (PSUBEB) ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati a faɗin jihar sakamakon fargabar tsaro da ta taso a kwanakin nan.

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za a rufe ƙananan makarantun sakandare tun daga Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, yayin da makarantun firamare za a rufe su daga Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025.

Wannan mataki na zuwa ne bayan sace ɗalibai a wasu makarantu da ke jihohin Kebbi da Neja a ‘yan kwanakin da suka gabata, abin da ya tayar da hankalin iyaye da hukumomi.

PSUBEB ta sanar da cewa rufe makarantun mataki ne na wucin-gadi domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na ɗaukar lafiya da tsaron ɗalibai da muhimmanci.

Hukumar ta buƙaci Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi, shugabannin makarantu da shugabannin al’umma da su ba da cikakken haɗin kai wajen aiwatar da umarnin, tare da zama masu kula da duk wata alama ta rashin tsaro a yankunansu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *