Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Laraba A Matsayin Hutu Don Bikin Ranar Samun ’Yancin Kai


Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025, a matsayin hutu don bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ’yancin kai.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya ’yan Nijeriya murna tare da buƙatar su ci gaba da nuna kishin ƙasa, haɗin kai da juriya.

Haka kuma ya buƙaci ’yan kasa da su mara wa  Shugaba Bola Tinubu baya, inda ya mayar da hankali kan farfaɗo da ƙasa, bunƙasa tattalin arziƙi, da ci gaba.

Ministan ya bayyana tabbacin cewa idan aka haɗa kai, Nijeriya za ta ci gaba da samun zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziƙi.

Ya yi wa ’yan Nijeriya fatan gudanar da biki mai cike da annashuwa, tare da kira da a yi tunani kan tafiyar da aka yi tun daga samun ’yanci, sannan a haɗa hannu wajen gina makoma mai kyau.




Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp





Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *