Abin da ya faru a zaman sulhun PENGASSAN da Matatar Ɗangote

[ad_1]



A ranar Talatar nan ake sa ran ci gaba da tattaunawa tsakanin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur (PENGASSAN) da Kamfanin Matatar Man na Ɗangote kan taƙaddamar da ke tsakaninsu.

Ana sa ran za a ci gaba da zaman sulhun, wanda Gwamnatin Tarayya ta kira domin sasanta ɓangarorin ne zuwa da yamma.

Hakan ta faru ne bayan an tashi taron a cikin tsakar daren ranar Litinin ba tare da an cimma wata matsaya ba.

Gwamnatin Tarayya ta kira zaman sulhun ne bayan ƙungiyar PENGASSAN ta zargi Kamfanin Ɗangote da kora da kuma sauyin aikin mambobinta kimanin mutum 800.

PENGASSAN ta yi barazanar yajin aiki muddin ba a dawo da ma’aikatan ba, a yayin da kamfanin ke cewa ga sallame su ne saboda suna masa zagon ƙasa.

Taron, ya samu halarcin shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, da wakilan Kamfanin Ɗangote, da sakataren TUC, Nuhu Toro, da wasu jami’an gwamnati. Ministan Kwadago, Maigari Dingyadi, ne ya jagoranci zaman tare da Ministan Kuɗi, Wale Edun.

A yayin jawabinsa na buɗe taron, Minista Dingyaɗi ya ja hankalin ɓangarorin cewa, “Abin da ke faruwa a yau yana da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziƙinmu da tsaron ƙasa. Mun samu labarin cewa PENGASSAN ta kira yajin aiki.”

Bayan awannin ana tattaunawa, wani wanda ya halarci zaman ya shaida wa wakilinmu cewa wakilan Kamfanin Ɗangote sun ƙi amincewa da dawo da ma’aikatan da aka kora, inda suka kira su “masu zagon ƙasa”, lamarin da ya fusata shugabannin ƙwadagon.

“An ba kowanne ɓangare damar gabatar da buƙatunsu, amma duk sun nace a kan matsayinsu. Babu wanda ya yarda ya sassauta,” a cewar majiyar.

NLC ta shiga lamarin

A gefe guda kuma, Ƙungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) ta tura saƙo ga ƙungiyoyinta, tana zargin Kamfanin Ɗangote da take-taken tauye haƙƙin ma’aikata da karya doka.

A wata wasika da Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya aika, ƙungiyar ta ce kamfanin na “ƙoƙarin karya ƙungiyoyi, bautar da ma’aikata da kuma wulaƙanta doka,” tare da yin iƙirarin cewa ya daɗe yana aiki “kamar wata gwamnati a cikin gwamnati.”

Wasikar ta umarci rassan ƙungiyar da su fara gaggawar shirya mambobi tare da shirin tunkarar rassan kamfanin a faɗin ƙasa kan abin da suka kira “tsaurin kai ga doka.”

Ƙungiyar ta bukaci su kafa kwamitocin wayar da kai cikin sa’o’i 72, tare da haɗin gwiwa da sakatariyar NLC.

“Wannan rashin ladabi na Ɗangote dole ne a tunkare shi da ƙarfi daga ɓangaren ƙwadago,” in ji wasikar.

“Da gumin ma’aikatan Nijeriya ne suka gina wannan kamfani; ba za mu bari ya zama ana zaluntar su ba. Tare muke tsaye, tare za mu yi nasara.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *