An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki
[ad_1]
Ma’aikatar ilimin Firamare da Sakandire a Jihar Sakkwato ta dakatar da shugabannin makarantun sakandire shida kan zargin rashin biyayya a wajen aiki tare da karbar kuɗaɗen sakamakon jarabawar kammala ƙaramar sakandire
Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandire na jihar, Farfesa Ahmad Ladan Ala ne ya bayar da umarnin dakatar da shugabannin makarantun.
Makarantun su ne makarantar sakandaren mata ta Nana Girls, makarantar sakandaren jeka- ka- dawo ta Gagi da sakandiren jeka- ka- dawo ta Mana, da sakandiren tunawa da Giginya da sakandiren Mana da kuma sakandiren jeka- ka- dawo ta Silame a bisa laifin rashin biyayya ga hukuma.
A kan hakan Kwamishinan ya kafa kwamiti mai wakilai biyar da zai gudanar da bincike kan zargin saɓa wa umarnin gwamnati a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mustapha Namakka Tukur.
A sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar Ibrahim Iya ya sanyawa hannu a ranar Juma’a ya ce ma’aikatar ta bayar da himma wajen tabbatar da gaskiya a dukkanin makarantu.
Ya ce ma’aikatar ta tsaya a kan tabbatar da ladabi da bin doka don haka babu wani shugaban makaranta da za a bari yana sabawa doka ko karbar kudade a hannun dalibai da iyaye ba tare da an hukunta shi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link