Kamfanonin Jamus Za Su Kara Zuba Jari Da Gudanar Da Kasuwancinsu A Kasar Sin

[ad_1]

A kwanakin baya, ziyarar shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz a kasar Sin ta samu nasarori da dama, kamar su daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannonin kyautata tsari tare da kiyaye muhalli, da kafofin watsa labaru da sauransu, da yin shawarwari tare da kamfanonin kasar Sin, da kuma kallon shirin wasan mutum-mutumin inji da aka yi gwaji a yayin shirye-shiryen shagalin CMG na bikin bazara na kasar Sin.

Game da ziyarar shugaba Merz, manajar sashen yankin gabashi da arewacin nahiyar Asiya na kamfanin Beiersdorf AG na kasar Jamus Xue Wei ta bayyana cewa, ziyarar ta shaida yanayin kasuwar kasar Sin mai kyau, lamarin ya alamta nasarorin da Sin ta samu a cikin shekaru 40 da aka yi kokarin raya kasar Sin, kuma an shaida cewa, za a ci gaba da more yanayin cinikayya cikin haske da adalci, kamfanonin kasar Jamus suna yin imani da kara zuba jari da gudanar da kasuwancinsu a kasar Sin cikin dogon lokaci. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *