Dalilan Da Suke Sa Mata Samun Ƙarin Mahaifa (Fibroid) (2)
[ad_1]
Ci Gaba Daga Makon Da Ya Gabata
8: Rashin ɓitamin D: ƙarancin ɓitamin D a jiki kan iya ta’azzara ciwon fibroid. Don haka ki fito riƙa fitowa kina shan hantsi da safe aƙalla na mintuna 30–40 a rana, ko ki sha ɓitamin D bisa shawarar likita.
9. Haihuwa: Matan da ba su taɓa haihuwa ba suna da yiwuwar samun fibroid fiye da waɗanda suke haihuwa. Haihuwa na taimakawa a wasu lokuta wajen rage haɗarin fibroid.
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci Matasa Su Riƙa Tantance Sahihancin Labari Kafin Su Yaɗa Shi
- Saka Wasu Kamfanonin Japan Cikin Jerin Kamfanonin Da Aka Hana Sayar Musu Da Kayayyakin Sin Mataki Ne Da Ya Dace
10. Hawan jini: Wasu bincike sun nuna cewa hawan jini na iya taimakawa wajen girman fibroid. Ki kula da BP ɗinki – ki rage gishiri, ki ci abinci mai kyau, ki riƙa motsa jiki.
11. Damuwa: Damuwa da wahala sosai suna rikita hormones a jiki, wanda zai iya kawo ciwo fibroid har su girma. Ki riƙa hutawa, ki rage damuwa, ki guji shiga damuwa, Lafiyar kwakwalwarki tana da muhimmanci sosai.
12. Muhalli da kike zaune: Wasu mayukan shafawar, da kayan kwalliya suna ɗauke da sinadarai masu kama da estrogen. (ɗenoestrogens).
Rashin Haihuwa:
Fibroid suna iya kawo matsala wajen samun ciki ko ɗaukar ciki har zuwa hana haihuwa.
Yadda suke kawo matsala:
Suna iya toshe bututu ko hannun mahaifa (fallopian tubes) su hana jaririn shiga cikin mahaifa . Suna iya canza suffar mahaifa, wanda ke hana jariri ya zauna daidai a ciki.
A wasu lokuta, suna hana jariri makalewa a jikin bangon mahaifa. Idan kina da fibroid kuma kin daɗe baki samun juna biyu ba, ki tuntuɓi likita domin a duba ki a baki maganin da ya dace dake ko a cire shi.
Fibroid ba sabon abu bane, amma ana iya
hana rage hadarin faruwar sa ta hanayar
Cin abinci mai kyau- Motsa jiki- Rage damuwa- Shan ɓitamin D- Kulawa da nauyi.
Zuwa Asibiti a duba lafiya lokaci zuwa lokaci. Shan magani kamar yadda likita ya umarta idan an samu kina da matsalar ta FIBROID.
[ad_2]
Source link