Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙorafin ɓangaren Turaki a PDP

[ad_1]



Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙorafin da tsagin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya shigar, tare da tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta rushe shugabancin da aka zaɓe shi a kai.

Kotun ƙarƙashin jagorancin alƙalai uku ta yanke hukuncin cewa ƙorafin da ɓangaren Turaki ya shigar ba shi da tushe, tana mai cewa Babbar Kotun Tarayya tana kan daidai lokacin da ta hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman ta Ƙasa (INEC) amincewa da babban taron ƙasa na PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.

Tun da farko Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci a ranar 31 ga Oktoba cewa taron jam’iyyar da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba a Ibadan — inda aka zaɓi Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar — bai gudana bisa ƙa’ida ba.

Sakamakon haka ne ɓangaren Turaki ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin, yana mai cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar domin batun ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyya.

Sai dai kotun ɗaukaka ƙarar ta yi watsi da wannan iƙirari, tana mai cewa masu ƙara suna da haƙƙin kai ƙara domin kare muradunsu na dimokuraɗiyya, kuma babu hujjar cewa an hana PDP damar kare kanta yadda ya kamata.

Kotun ta kuma ci tsagin Turaki tarar naira miliyan biyu kan shigar da ƙarar da ta ce ba ta da tushe, tare da cewa za a ci gaba da sauraron wasu batutuwan da suka shafi rikicin cikin gida na jam’iyyar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *