Mafarkin Kasashen Afrika Zai Tabbata Albarkacin Kasar Sin
[ad_1]
A lokacin da taro na 4 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, wadda ke zaman majalisar dokokin kasar ke gudana a birnin Beijing, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kira taron manema labarai a jiya Lahadi, inda ya yi karin haske kan manufofin diplomasiyyar kasar Sin.
Mun riga mun san cewa, burin kasar Sin har kullum shi ne, zaman tare bisa adalci da daidaito da hakuri da girmama juna da kuma samun ci gaba na bai daya a duniya.
Da aka yi masa tambaya game da irin sabbin ci gaban da za a gani a dangantakar Sin da Afrika a bana, Wang Yi ya bayyana wasu batutuwa 3:
Na farko, al’umma mai makoma ta bai daya ta Sin da Afrika. Wannan na nufin bangarorin biyu sun zarce abokan hulda kawai, abokai ne da za su rika tafiya tare kafada da kafada a kan tafarki daya na samun ci gaba. Haka kuma yana nufin Sin za ta kasance babbar yaya wajen jagorantar kasashen Afrika su lalubo hanyar da ta dace da su ta samu ci gaba da kuma dogaro da kansu. Wannan ya nuna cewa, Sin tana son kasashen Afrika su kasance masu tsayawa da kafarsu, masu karfin fada a ji kan lamuran da suka shafe su, haka kuma masu bijerewa baba-kere da cin zali. Wanda zai taimaka matuka wajen ganin sun amfanawa kansu da kansu ba tare da neman taimako mai tattare da sharuda da katsalandan ba.
Batu na biyu shi ne, soke harajin kwastam. A duniyar dake fama da rikicin cinikayya da karuwar harajin fito, ba tare da la’akari da matsayin kasashen Afrika na masu tasowa ba, Sin ta kara nuna matsayinta na babbar yaya, ta soke haraji kan kayayyakin kasashen Afrika 53 dake da huldar diplomasiyya da ita. Abun nufi, kasar Sin ta bude kofarta da katafariyar kasuwarta ga kasashen Afrika su shigo su ci gajiya. A ko da yaushe burin kasashen shi ne, su tashi daga masu dogaro da kayayyaki daga kasashen waje, su zama masu sarrafawa da fitar da kayayyaki. Kuma a bana, mafarkinsu zai tabbata albarkacin kasar Sin. Wannan abu ne da zai karfafa takardun kudinsu da bunkasa masana’antu da ayyukan gona, wadanda za su samar da aikin yi. Idan hakan ta samu kuma, arziki zai wadata a cikin al’umma, kuma za a samu raguwar aikata laifuka da tabbatuwar zaman lafiya.
Batu na 3, aiwatar da shirye-shirye 600 na musayar al’adu tsakanin Sin da Afrika. Fahimtar juna ita ce kashin bayan kowane mu’amala. Yayin da ake samun habakar hulda ta cinikayya da tattalin arziki, ya zama wajibi a fahimci juna tsakanin mabambantan al’ummomi domin kaucewa rigingimu. Musaya tsakanin Sin da Afrika za ta bayar da muhimmiyar gudunmawa ga burin gina al’umma mai makoma ta bai daya. Za ta kara kyautata mu’amala tsakanin al’ummominsu, haka kuma, za ta toshe duk wata kafa da masu yada jita-jita ke amfani da ita ta haddasa fitina.
Idan muka nazarci wadannan batutuwa da ya zayyano, a dunkule abubuwa ne da za su inganta ci gaban kasashen Afrika da bude musu kofar samun karin wadata. Hakika ci gaban Sin, ci gaba ne ga nahiyar Afrika. Kasar Sin ta zama jagora mai haskawa kasashen Afrika hanyar samun ci gaban da suke buri. (FMM)
[ad_2]
Source link