’Yan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 11 a Zamfara

[ad_1]



Wasu ’yan bindiga da ake zargin sun shigo cikin al’umma sanye da hijabai sun yi garkuwa da mutane 11 ciki har da masallata guda uku a Jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadin da ta gabata a garin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru, kamar yadda rahotanni daga shafin Zagazola Makama suka tabbatar.

Makama wanda kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya ne ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne sanye da hijabai da rigunan mata da suka yi basaja da su, inda suka yi awon gaba da mutane takwas suka tsere cikin jeji.

“Dakarun sojoji da ‘yan bijilanti sun bi sawunsu, amma ba su samu nasarar kama su ba,” in ji wata majiya.

“Daga baya an tsinto wata jaka dauke da rigunan mama da hijabai da suka yi amfani da su wajen ɓatar da kama,” a cewar majiyar.

A wani lamarin mai nasaba da wannan, wasu ‘yan bindiga sun kutsa cikin garin ‘Yarlaluka da safiyar Lahadin da ta gabata, inda suka tarwatsa wasa masallata a masallaci sannan suka yi garkuwa da mutum uku.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Dan Asabe Alhaji Garba, tare da wasu mutum biyu da ke tare da shi a lokacin harin.

Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan bindigar sun shiga garin salin-alin ba tare da wata fargaba ba, abin da ke nuna yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a yankin, duk da ikirarin hukumomi na yi wa tufkar hanci.

Sai dai daga baya, jami’an tsaro sun kaddamar da bincike a yankin, inda suka cafke mutane shida da ake zargin suna da alaka da hare-haren da kuma garkuwar da aka yi, da yanzu haka ana ci gaba da titsiye su a hannun hukumomin tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *