APC ta lashe zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa a Kano
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kano.
Da yake sanar da sakamakon da misalin karfe 6:10 na safiyar Lahadin nan, babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Muhammad Waziri na Jami’ar Bayero, ya bayyana Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’u 31,472.
Garba Gwarmai ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Yusuf Ali Maigado wanda ya samu ƙuri’u 27,931.