Burin Sin Na Neman Ci Gaba Ya Samar Da Damammaki Ga Duniya
[ad_1]
Jiya Alhamis, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da rahoton aiki ga majalisar wakilan jama’ar kasar wato NPC, kuma bisa rahoton, kasar Sin na sa ran samun karuwar ma’aunin tattalin arziki na GDP da kaso 4.5 zuwa kaso 5 a bana, tare da jaddada cewa, za ta yi kokarin cimma hakan a aikace.
Bisa shirin raya tattalin arzikin kasar Sin, burin neman bunkasuwar tattalin arziki na bana ya dace da jadawalin raya tattalin arzikin kasar zuwa shekarar 2035, ya kuma dace halin da ake ciki, wanda ya kuma nuna yadda aka yi hangen nesa. Kana, hasashen da masana suka yi ya nuna cewa, ya zuwa shekarar 2035, idan kasar Sin tana son cimma burinta na samun karuwar ma’aunin GDP da ya ninka sau biyu bisa na shekarar 2020, tare da kai wa matsayin kasa mai matsakaicin ci gaba, ya kamata, Sin ta tabbatar da samun karuwar ma’aunin tattalin arziki na GDP da sama da kaso 4.17 bisa dari kowace shekara cikin shekaru 10 masu zuwa a jere. A bana kuma, gwamnatin kasar ta tsara wani burin da ya zarce kaso 4.17 bisa dari, wanda ya dace da bukatun kasa na dasa tushe mai karfi, da dukufa wajen raya dukkannin fannoni a tsakanin shekarar 2026 zuwa shekarar 2030, wato lokacin da za a aiwatar da daftarin shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arzikin kasa da zamantakewar al’umma karo na 15.
Ban da haka kuma, cikin rahoton aikin gwamnati na bana, an gabatar da manufar gaggauta aikin raya sabbin sana’o’i da gaggauta aikin raya kimiya da fasaha, lamarin da ya dace da halin da ake ciki na neman bunkasuwar kimiyya da fasaha.
A sa’i daya kuma, an ce za a mai da hankali wajen raya sana’o’in bayar da hidima ta fuskar habaka kasuwanni da kara bude kofa ga waje, tare da fadada harkokin zuba jari, da kyautata tsarin cinikayyar waje, da gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” yadda ya kamata da dai sauran matakai, lamarin da ya nuna aniyar kasar Sin ta kara bude kofa ga waje bisa manufofi, da kara musaya a tsakanin kasashen duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link