Sin Ta Fadada Yawan Biranen Gwajin Cinikayyar Kasa Da Kasa A 2026
[ad_1]
Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce a shekarar nan ta 2026, gwamnatin kasar Sin ta fadada adadin biranen gudanar da gwajin cinikayyar kasa da kasa zuwa 45 daga 25 da ake da su a shekarar 2025.
Da take tsokaci dangane da hakan yayin taron masu ruwa da tsaki a jiya Litinin, shugabar hukumar Sun Meijun ta ce, birane 20 da aka kara cikin shirin sun hada da Hohhot, da Changchun, da Suzhou, da Jinhua, da Quanzhou. Sauran su ne Nanchang, da Yantai, da Wuhan, da Changsha, da Zhuhai, da Nanning, da Kunming da kuma Xi’an.
Sun ta ce, karkashin wannan manufa, za a kaddamar da sabbin matakai, wadanda za su karkata ga daga matsayin cinikayyar hajoji, da fadada cinikayyar hidimomi, da ingiza ci gaban cinikayyar dijital da hajoji marasa gurbata yanayi.
Kazalika, matakan za su kunshi na aiwatar da kirkire-kirkire a ayyukan kwastam, a fannin sanya ido ga ayyukan tantance kayayyakin shige da fice, da inganta hidimomi ga sabbin fannonin cinikayyar waje, da kyautata hidimomin safarar hajoji tsakanin kan iyakoki, da gina tashoshi na zamani, da inganta mizani zuwa matakin kasa da kasa, da kuma kyautata goya baya ga kamfanoni. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link