Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Tabbatar Da Sauyin Da Zai Haifar Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya, In Ji Shugaban WBCSD
[ad_1]
An bayyana kasar Sin a matsayin karfi mai muhimmanci dake jagorantar duniya zuwa ga tafarkin samun sauyin da zai haifar da ci gaba mai dorewa, haka kuma akwai yuwuwar za ta taka muhimmiyar rawa a mataki na gaba na samar da ci gaba mai dorewa a duniya.
Peter Bakker, shugaban kungiyar kamfanoni masu rajin samar da ci gaba mai dorewa ta kasa da kasa (WBCSD) ne ya bayyana haka, cikin wata rubutacciyar hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron dandalin tattauna tattalin arzikin duniya na Davos a kasar Switzerland. Peter Bakker ya kuma zayyano wasu haddura 3 da duniya ke fuskanta da suka hada da mummunan tasirin sauyin yanayi na zahiri dake kawo tsaiko ga ayyukan samar da kayayyaki da zuba jari da rarrabuwar kawuna tsakanin yankuna dake illa ga cinikayya da tsarin samar da kayayyaki da kuma sauyi na gaggawa da ake samu a fannin fasahar zamani kamar kirkirarriyar basira ta AI, da saurinsa ya zarce na harkokin shugabanci da kuzarin ma’aikata.
Ya ce abun da ya kamata duniya ta mayar da hankali kai shi ne, hada jari da manufofi da matakan kasuwanci ta yadda za su gaggauta komawa ga harkokin da za su rage fitar da hayakin carbon da aiwatar da manufofi masu alfanu ga muhalli da kuma fadada dabarun kasuwanci.
Ya ce Sin misali ce ta kasar dake samun sauyi cikin nasara. Ya bayyana ta a matsayin mai taka rawa uku da suka hada da zama cibiyar kere-kere da muhallin kirkire-kirkire mai samun ci gaba cikin sauri, haka kuma jagora a fannin fasahohin samar da makamashi mai tsafta. Ya ce wadannan karfi da take da su, na tsara wa duniya hanyoyin rage fitar da hayakin Carbon. (FMM)
[ad_2]
Source link